Wani Tsohon Gwamna Na Shirin Komawa APC
Cif Olusegun Osoba, wani tsohon gwamna ta jihar Ogun na shirin komawa jam’iyyar APC bayan da suka gudanar da jerin tattaunawa da shugabannin jam’iyyar.
Cif Olusegun Osoba, tsohon gwamnan jihar Ogun
Cif Osoba wani tsohon gwamna ta jihar Ogun ne ya gita daga jam’iyyar ta APC inda ya koma SDP saboda sabanin ra’ayi da suka samu da Bola Tinubu da kuma gwamnan Jihar Ogun yanzu, Sanata Ibikunle Amosun.
Ya bayyana cewa suna tattaunawa ne akan lamurra da yawa domin ciyar da yankin gaba.
Ya bayyana cewa: “Su (Dalilan sabanin namu) na cikin abubuwan da muke tattaunawa akai. Ni mai so cigaba be sai yasa a ko’ina nike ina tare da masu cigaba.”
The post Wani Tsohon Gwamna Na Shirin Komawa APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.