Tsagerun Nija Delta Sun Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 30
Wata kungiya marar suna tsagerun Nija Delta ta ba gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kwanaki 30 data saki Nnamdi Kanu ko dasu fara ta’addanci.
Tsagerun Nija Delta
Jaridar The Breaking Times ce ta kawo labarin inda take bayyana cewa Jami’in kungiyar ne, mai suna, General Ben ya bayyana haka.
Ya bayyana cewa abunda Nnamdi Kanu yake yi abune mai kyau, babu wani dalilin da zaya sanya a cigaba da tsare shi. Ya gargadi gwamnati da cewa idan har wa’adin ya cika ba’a sake shi ba, toh zasu fara da sace fararen fata yan kasar waje domin nuna ma gwamnati abunda zasu iya.
Ya bayyana cewa komin yawan sojojin da za’a kawo baza ya razana su ba. Sannan kuma ya tunatar da gwamnati akan irin ta’addanci da sukayi a baya.
The post Tsagerun Nija Delta Sun Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 30 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.