Manyan labarai 8 na ranar Laraba
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 8 wadanda sukayi fice a ranar Laraba 9 ga watan Maris. Ku duba domin ku same su.
1. An dakatar da Shari’ar Nnamdi Kanu
Saboda ya roki kotu a dakatar da Shari’ar sa ya sanya aka dakata
2. NNPC na yajin aiki saboda Buhari
Domin yace a raba ta gida 7 ya sanya suka shiga yajin aiki.
3. Sojin sama tayi luguden bama bamai ga Yan Boko Haram
Rundunar task force ta 121 tayi luguden bama bamai ga yan Boko Haram
4. Magoya bayan Biafra sunyi ma Okorocha wulakanci a Ingila
Inda yaje domin yayi magana a Chattam House, magoya bayan Biafra sunyi mashi ihu.
5. Mata sunyi zanga zanga a Legas
Saboda rashin tsaro a Legas ne ya sanya su suka yi zanga zangar.
6. Mutane 34 sun rasu bayan da bane ya fadi a Legas
Mutane 34 ne suka mutu bayan da wani bene mai hawa 5 ya fadi a Legas
7. Buhari zaya ziyarci Amurka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya ziyarci Amurka inda zasu tattauna akan ma’adanin Nuclear
8. Majalisar wakilai ta amshe ikon Majalisar Kogi
Saboda suna yawan rigima ne ya sanya majalisar wakilai ta amshe ikon majalisar Kogi bisa ikon da kudun tsarin mulki na 1999 sakin layi na 11 ya basu.
The post Manyan labarai 8 na ranar Laraba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.