Yan fashi sun farma Yar Jarida
– Yan fashi sun farma yar jarida
– Sun amshe mata kudade
– Sun kusa yi mata fyade
Toyin Ibrahim, Yar Jaridar da akayi fashi
Toyin Ibrahim, wata yar jarida dake aiki da gidan talabijin na TVC ta tsallake rijiya da baya.
Ita da wasu pasinjoji ne suka shiga wata motar haya a Ketu dake jihar Legas, ashe masu motar yan fashi ne. Bayan sun amshe masu kudaden su kuma sai suka nemi suyi mata fyade.
Wannan ya faru ne da misalin karfe 5 da rabi akan hanyar su ta Berger-Magado. A lokacin hada wannan rahoto, yar jaridar na a wani asibiti a Magado inda ake duba ta bayan da ta samu wasu raunuka a jikin ta.
KU KARANTA; Rikicin majalisar jihar Kogi
” Kimanin minti 2 bayan shigar mu mota sai naji ana bugu na. Sai aka ce in bada katin ATM, sai na basu na karya. Da suka duba sai suka ce na karya ne inda suka taru kaina cikin motar mai kujeru 14. A nan ne nima na bugi wani. Sai a fara kokarin yaga mani kaya zai yi mani fyade.
” Inda sunyi mani fyade da mutuwa zanyi. Bayan da suka gama amshe mana kudade sai suka jefo mu kasa.
The post Yan fashi sun farma Yar Jarida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.