An kama Yan Boko Haram 3 a Kamaru
Rahotanni daga kasar Kamaru na nuna cewa an kama masu kaima Boko Haram kayan da suke amfani dasu.
A cewar Cif Bisong Etahoben, wani dan jarida mai bincike na Kamaru, an kama masu kaima kungiyar kayan abinci ne a ranar 9 ga watan Maris na 2016.
KU KARANTA: Sojoji sun kashe yan Boko Haram 16 a Pulka
A jerin sakonni daya aiko a shafin shi na Twitter, ya bayyana cewa shugana yan banga na garin Gangwa, Alhaji Brahim, ya rasu sakamakon arangama da sukayi da kungiyar Boko Haram a ranar Alhamis.
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun farma garin Bita
A kwanakin nan sojojin Najeriya wadanda suke yaki da Boko Haram na Opertaion Lafiya Dole sun samu nasarori akan kungiyar wanfa ya sanya yanzu bata iya kai wani hari a Maiduguri da kewaye
The post An kama Yan Boko Haram 3 a Kamaru appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.