Buhari ya canza ma’aikata 184
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza ma’aikata 184
– Ma’aikatan ana zargin su da canza kasafin kudin Najeriya na 2016
– Ya sha alwashin hukunta su
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin canza manyan ma’aikata guda 14 daga ofishin kasafin kudin kasa. Umurni ya bayyana cewa duka su bar Ofishin a jiya kuma su kuma sabbin wuraren aiki da aka kaisu.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wani jami’i ya bayyana mata cewa, duka wada manya ma’aikatan hukumar wannan umurni ya sahfe su. Kuma shugaba Buhari ya jadda cewa dole zuwa ranar Juma’a kowa ya koma sabon wurin aikin shi.
KU KARANTA: Ma’aikatan APC sun maganta akan albashin su
Shugaba Buhari ya sha alwashin hukunta masu hannu cikin canza kasafin kudin kasa inda ya bayyana cewa tun daga lokacin soja har na farar hula bai taba jin inda wasu suka zauna suka canza kasafin kudin kasa ba. Ya sha alwashin hukunta masu hannu a ciki da hukunci mai tsanani.
The post Buhari ya canza ma’aikata 184 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.