Kotun CCT ta daga shari’ar Saraki
– Kotun CCT ta daga shari’a Bukola Saraki
– Ta maida shari’ar zuwa 18 ga watan Maris na 2016
A cigaba da shari’ar shugaban majalisar dattawa da aka cigaba a yau juma’a 11 ga watan Maris, Alkali mai shari’ar Umar Danladi ya dage shari’ar inda ya maida ta zuwa 18 ga watan Maris.
KU KARANTA:
An dakatar da karar Bukola Saraki |
Wannan yazo ne bayan da Lauyan Bukola Saraki, Kanu Agabi, ya kalubalanci ingancin kotin tayi ma shugaban majalisar shari’a. Wannan na zuwa ne bayan da Saraki ya kai kotun ta CCT kotun daukaka kara da kotun Koli inda ya roke su da su hana kotun CCT bincikar shi. Amma duka kotuna sun bayyana cewa kotun CCT nada hurumin da zata bincike shi kuma bisa ka’ida aka kafa ta.
Lauyan gwamnati, Rotimi Jacobs ya bayyana cewa a shirye suke da su kawo shaidu wadanda zasu shaida cewa Saraki yayi bayyana kaddarorin shi kamar yadda doka ta tanada a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara, tsakanin 1999 zuwa 2007.
Idan za’a iya tunawa daga farko Saraki kin yin biyayya yayi gakotun ta CCT a lokacin data bukaci yazo, sai da tayi barazanra kama shi sannan ya gurfana a gaban ta.
The post Kotun CCT ta daga shari’ar Saraki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.