Layin mai zaya kare nan da kwana 2 – Kachikwu
– Karamin Ministan mai na Najeriya ya ba Yan Najeriya hakuri saboda rashin mai
– Yayi alkawarin kawar da layukan mai a cikin kwanaki 2
Karamin Ministan Mai. Mr Ibe Kachikwu
Karamin Ministan Mai na Najeriya ya bi bayan shugaba Buhari inda ya ba Yan Najeriya hakuri akan rashin mai. Ya kuma sha alwashin cewaa duka layukan mai zasu kare a cikin kwanaki 2.
KU KARANTA: Shugaba Buhari zaya tafi Malabo
Mr Ibe Kachikwu ya bayyana haka ne a lokacin da yake ziyarar wasu gidajen mai a Abuja inda ya bayyana cewa NNPC tayi kari inda yanzu kimanin tankokin mai 300 ke kawo ma Abuja mai kullum.
Kachikwu Yace ” Da akwai isassu mau kawo mai, yajin aikin nan da akayi ya shafe mu ssai, zaya dauki lokaci kafin layin mai ya bacce. Amma yanzu suna aiko da mai isasshe. Nan da kwanaki 2 layin mai zaya bacce”
KU KARANTA: An kama mijin tsohuwar Ministar Mai
“ Ina mai baku hakuri. Babu wanda keso ya tsaya layi mai har na awa biyu. A yanzu muna magana da CBN domin ta taimaka ma masu kawo mai a Najeriya. NNPC na iya bakin kokarin ta, kayan man ne kawai basu isa ba”
Idan za’a iya tunawa, kwana daya daya wuce, Tokumbo Korode, shugaban NUPENG na kudu maso yamma, ya bayyana cewa kila a cigaba da ganin layukan mai har zuwa karshen wannan watan.
Masu abubuwan hawa na fuskantar wahala wajen samun Mai. Haka zalika wutar lantarki tayi karanci saboda bubutun iskan gas da ake fasawa a wasu yankuna na Nija Delta a wadannan kwanakin.
The post Layin mai zaya kare nan da kwana 2 – Kachikwu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.