Shugaba Buhari zaya tafi Malabo
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya tafi Malabo
– Zaya tattauna da shugaba Nguema
– Zasu sanya ma yarjejeniya tsakanin kasashen 2 hannu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari za yayi tafiya daga Najeriya inda zaya tafi Malabo, babban birnin kasar Equatorial Guinea. Shugaban kasar za yayi wannan tafiya ne a ranar Litinin 14 ga watan Maris. A cewar Femi Adesina.
KU KARANTA: Buhari ya nada Mrs Adejoke mai bashi shawara
Shugaban kasar zaya samu tattaunawa da shugaban kasar Guinea, Obiang Nguema Mbosogo domin a samu yarjejeniya akan sha’anin tsaro. A shekarar data wuce ya kamata ace kasashen ECOWAS dana ECCAS ya kamata ace sunyi taron, amma saboda zaben Najeriya ya sanya aka daga taron.
Ana sa ran shugaban kasa Buhari da Shugaba Nguema zasu sanya hannu akan kara satar mai daga Nija Delta. hada yan sanda masu kula da iyakar ruwa ta kasashen guda 2, da kuma hana satar fahimta tsakanin kasashen 2.
Babban muhimmin abu da za’a tattauna a taron shine hana yan ta’adda shia yankunan guda 2 da kuma hada gwiwa domin kawo karshen ta’addanci ga yankunan guda 2.
KU KARANTA: Buhari ya canza ma’aikata 184
Shugaba Buhari zaya samu rakiya daga Ministan tsaro, Mansur Dan Ali mai, Mai ba shugaban kasa shawara akan tsaro, Babagana Munguno, da sauran jami’an gwamnati. Ana sa ran a ranar Talata shugaban kasa zaya dawo
The post Shugaba Buhari zaya tafi Malabo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.