Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Март
2016

Ma’aikatan NAICOM na zanga-zanga saboda Ministar Kudi

0

– Ma’aikatan hukumar NAICOM na zanga-zanga

– Suna zargin Ministar kudi da aikata rashawa

Takardun da ma’aikatan hukumar sukayi zanga zanga dasu

Ma’aikatan hukumar NAICOM sunyi zanga-zanga a yau Litinin 21 ga watan Maris, a hedikwatar su dake Abuja.

Ma’aikatan hukumar kamar ma’aikatan hukumar NAICOM suma, duka suna neman a binciki shugabannin hukumomin akan aikata rashawa.

Hedikwatar ma’aikatar na nan akan hanyar Ladoke Akintola dake a birnin tarayya, Abuja.

Ma’aikatan hukumar sun kulle hukumar a yau da safe da misalin karfe 8 inda suka nemi mataimakin shugaban hukumar mai kula da aiyuka da kudade Mr George Onekhena daya sauka.

Masu zanga-zangar sun zo ne a karkashin gamammiyar kungiyar AUPCTRE inda suka nemi a gudanar da bincike akan manyan hukumar domin ceton ta daga rushewa.

Ma;aikatan hukumar sun zargin manyan hukumar da tafiyar da hukumar ta NAICOM kamar kamfanin su da suka hada da kamsu.

Wasu daga cikin ma’aikatan hukumar NAICOM da sukayi zanga zangar zaune a gefe

An hana masu zanga-zangar shiga harabar hukumar inda su kuma suka kulle ta suka sha alwashin hana manyan hukumar shiga cikin ta.

Inda yake magantawa, Ibrahim Abdullate, wanda shine shugaban masu zanga-zangar a karkashin gamammiyar kungiyar ta AUPTRE, ya zargi Ministar kudi, Kemi Adeosun, da karya ka’idar aiki inda ta nada wani matasi wanda ya gama jami;a a matsayin darakta a hukumar.

Shugaban masu zanga-zangar kuma ya zargi shugabannin hukumar da hana ma;aikatan hukumar samu  karin girma a ma’aikatar. yayi kira da a gudanar da bincike domin kawo karshen wadannan matsalolin.

A lokacin da ake hada wannan rahotan, masu zanga zangar sun tsaya gaban hukumar inda suke waken kungiyar kwadago. Wasu kuma sun koma gefe suna tattaunawa akan wasu lamurra.

Idan za’a iya tunawa, a lokacin da aka rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Mayu na shekarar 205, shugaban kasan ya sha alwashin kauda rashawa a Najeriya.

The post Ma’aikatan NAICOM na zanga-zanga saboda Ministar Kudi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса