Manyan labarai guda 9 wadanda sukayi fice a ranar Laraba
Naij.com ta tattara mau manyan labarai guda 9 wadanda sukayi fice a ranar Laraba 23 ga watan maris. Ku duba domin ku samu manyan labaran.
Shugaba Buhari a gaban majalisa da manyan jami’an gwamnati a lokacin da ya gabatar da kasafin kudin
1. Majalisar Dattawa Ta amince da kasafin kudi
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudin shekarar 2016
2. EFCC ta gurfanar da Tompolo kotu
Duk da cewa baya nan, hukumar EFCC ta gurfanar da Tompolo kotu akan zargin damfarar naira Biliyan 35 da yayi.
3. Zaben Rivers: Dan takara ya nemi jami’in hukumar zabe ya maido mashi da kudin shi
Domin yaci zabe, Azubuike Nwajoku na APC ya nemi wani jami’in hukumar zabe daya maido mashi da kudaden daya bashi na rashawa.
4. An kama yan manyan yan Boko Haram guda 2
An kama wasu manyan kwamandojin Boko Haram guda 2 a jihar Taraba
5. Shari’ar saraki: Lauyoyi sun nemi Alkali mai shari’a yayi watsi da sauraron karar
Wasu Lauyoyi a karkashin inuwa Lauyoyi masu rajin kare Damakaradiyya sun nemi Alkali Umar Danladi daya kori karar Saraki
6. Mutane 10 wadanda suk taimaki Buhari ya zama shugaban kasa
Naij.com ta fidda jerin manyan mutane 10 wadanda suka taimaki Buhari ya zama shugaban kasa
7. Jami’in tsaro ya gargadi gwamnatin Najeriya
Wani jami’in tsaro mai suna Dakta Ona Ekhhomu ya bayyana cewa kungiyar AlQaeda naso ta kaima Abuja da Legas hari.
8. Wike ya kai ziyarar ta’aziyya ga sojin Najeriya
Saboda wani Manjo da aka kashe da wasu sojoji guda 3, gwamna Nyesome Wike ya kai ziyarar ta’aziyya ga hukumar soji.
9. Jaridar Financial Times ta zargi gwamnatin Najeriya
Ta bayyana cewa shugabanin Najeriya suna rayuwa mai tsada alhali talakawa na wahala.
The post Manyan labarai guda 9 wadanda sukayi fice a ranar Laraba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.