– Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana wanda Shugaba Muhammadu Buhari wani mutum mai gaskiya ne
– Ango Abdullahi ya maganta kuma wanda Shugaba Buhari bashi da mutane masu kyau ba a karkashin gwamnatin tarayya
A hirar da ya yi da Muryar Amurka a Bauchi, wanda jaridar Rariya ta buga, Farfesa Ango Abdullahi wanda shi ne kakakin kungiyar dattawan Arewa ya ce ba’a mugun sarki sai mugun bafade saboda mutanen da suke kewaye da Shugaba Muhammad Buhari, yawancin su ba masu nagarta ba ne.
Farfesa Ango Abdullahi
Ya kara da cewa yawancin shugabanni masu mulki suna ganin su ne suke da iko kowa kuma suka kira ya yi aiki da su dole ne ya zama dan amshin shatansu, dalili ke nan da ake samun kurakurai.
Sannan kuma ya kara da cewa wadanda aka dauko su yi aiki ‘yan daukowa ne ba su kware da aikinsu ba. Yawancinsu ba su shirya fuskantar aikin da aka daukosu su yi ba.
Farfasa Ango Abdullahi wanda yake ganin mataimakan shugaban kasa yawancinsu ba su da nagarta ya yaba da yaki da cin hanci da rashawa da Shugaba Buhari ke yi amma mutum daya baya zama shi ne gwamnati. Dole ne ya yi aiki da wasu. Mutum daya baya zama gwamnati kuma ya yi nasara. Shugaba ya yi shugabanci amma ya tara mutane da suka san abun da suke yi ya yi aiki dasu.
Yaki da cin hanci da rashawa daidai ne amma ba shi kadai ba ne aikin gwamnati. Aikin gwamnati ya wuce karban kayan da aka sata. Yace shi a ganinsa shugaba Buhari bashi da mataimaka na kwarai da zasu taimakeshi da aikinsa.
Farfesa Abdullahi ya ce mafita ita ce shugaba ya sa ido kan masu aiki tare da shi. Ya tabbatar ma’aikata ne na kwarai. Sun san aikin da suke yi kuma masu gaskiya ne. An san shugaban mai gaskiya ne to sai kuma masu goya masa baya cewa su ma irinsa ne. Akwai alama su masu iyawa ne ko kuma masu kokari ne.
Shugaban ya riga ya fada cewa yana samun cikas daga fannin shari’a. Farfesa Abdullahi yace dama akwai sassa manya uku. Akwai fannin shari’a. Akwai fannin majalisa da kuma fannin zartaswa da shi shugaban yake yiwa jagoranta. Ya ce dole wadannan bangarorin uku su san gwamnati ba za ta samu nasara ba sai sun hada kai sun yi aiki tare.
Компании Псковской области чаще приглашают на работу соискателей из своего региона — аналитики
Два автобуса столкнулись на северо-востоке Москвы, движение перекрыто
Карпин о «Динамо»: «У нас нехватка кадров, так скажем. Говорить про “довольны”, “недовольны” — мне надо командой заниматься. А трансферная кампания — прерогатива клуба. Кто&nbs
Сахар на вес золота: как изобретение инсулина изменило медицину