Lauyan gwamnatin jihar Kaduna ya maganta akan yan kungiyar Shia
– An rahoto wanda wani lauyan gwamnatin jihar Kaduna yake wanda an mika makaman da aka samu a hannun yan kungiyar Shia wajen kwararru a jihar Legas domin bincike
– Kungiyar yan Shia ta musanta zargin aka ta inda take cewa wanda sojojin Najeriya na shirin dasu kai mana farmaki
Wani dan jaridar a jihar Kaduna mai suna Ibrahim Ammani ya ruwaito wanda, wani Kotun Majistare ta Kaduna wacce ke saurarar shari’ar ‘yan Shi’a wadanda ake tuhuma da tayar da tarzoma a rikicin daya barke tsakanin Sojoji da ‘Yan Shi’an a watan Disambar Bara, karkashin jagorancin Mai Shari’a Awwal Musa, a zaman da Kotun tayi a ranar Talatar data gabata a gidan Yarin Kaduna, ta saurari koke daga bakin Lauyan ‘yan Shi’a, inda ya bukaci da a bada belin wasu ‘yan Shi’an su biyar wadanda ke fama da rashin lafiya da kuma karancin shekaru.
Wata mata a karkashin kungiyar yan Shia
Barista Husaini Ibrahim yace wasu daga cikin yan Shi’an da yake karewa, suna fama da rashin lafiya da kuma wasu yara kanana wadanda basu balaga ba, inda ya nemi kotun data gaggauta bada belin su, domin samun kulawa ta musanmam.
KU KARANTA KUMA: Sani ya bayyana akan auren jinsi ko auren dabbanci
A martanin daya bayar, Lauyan Gwamnati Barista Abdullahi Bayero ya bayyana cewar hanya guda da ake tantace cewa Fursuna na fama da rashin lafiya ita ce takardar sanya hannun jami’in lafiya wacce ke bayyana cewar lallai wanda ake tsare dashi yana fama da rashin lafiya, domin a dokokin shari’a baya halasta a cigaba da tsare Mutum bayan yana fama da rashin lafiya.
Barista Bayero ya kara da cewar rundunar Soji ta mika makaman data amshe a hannun ‘yan Shi’an zuwa birnin Lagos domin gudanar da binciken kwararrru akai, saboda samun kyakkyawar madogara. Alkalin Kotun Mai Shari’a Awwal Musa ya dage zaman Kotun har ya zuwa ranar 26/04/16 domin cigaba da sauraren shari’ar.
A wani labarin makamacin hakan, Kungiyar ‘yan Shi’an ta fitar da wata takardar sanarwa wacce ta samu sanya hannun jami’in yada labarai na kungiyar Ibrahim Musa, inda ta bayyana cewar da akwai wani shiri da Sojoji suke da shi na kai farmaki akan ‘yan Shi’an a fadin Kasar nan, inda suka bayyana yunkurin Sojoji na kai hari akan’yan Shi’a a birnin Katsina ranar Mauludin Fatima, sannan suka nanata matsayinsu na a saki Zakzazky.
The post Lauyan gwamnatin jihar Kaduna ya maganta akan yan kungiyar Shia appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.