Sanata Shehu Sani ya bayyana akan auren jinsi ko auren dabbanci
– Akwai wani labari daga Musa Badayi, wanda ya rubuto akan amsawar Sanata Shehu Sani akan auren jinsi ko auren dabbanci
– Sanata Sani yana tsakanin sanatoci guda uku wadanda suke wakilta jihar Kaduna a majalisar dattawan Najeriya a Abuja
– Wani sanata yana tsakanin mutane wadanda suke yaki na hakkin bil adama a Najeriya
Da yawan mutane suna jifan Shehu Sani da maganganu irin na batanci, akan cewa yana goyan bayan auren jinsi da sauransu. Wannan mummunar magana ce ga mutun kamar Shehu Sani, wanda yake wakiltar Kaduna, ta tsakiya. Da yawan mutane suna fakewa da wasu dalilai marasa tushe bare makama.
KU KARANTA KUMA: Kungiyar Izala ta ziyarci kasuwar Abubakar Rimi
Ni zan kawo hujja karara, inda Shehu Sani ya yi jifa da suren jinsi. Su kuma ina so su kawo hujja karara inda Shehu Sani ya goyi bayan auren jinsi.
Sanata Shehu Sani
“Dabi’ar uren jinsi da luwadi da ta bayyana a kasashen Turai ta yamma, mu nan za mu ci gaba da la’anar wannan dabi’ar. Domin hakan ya sabawa dabi’unmu, ya kuma sabawa halayenmu. Hakan ma ya sabawa dabi’un mutane. Saboda dabi’a ce ta dabbancine.
“Aure na halak wanda bai sabawa mutuntaka ba shine tsakanin namiji da mace. Duk ko inda ka ga an zo da sabanin haka akwai matsala babba. Domin ko cikin dabbobi jinsin maza, mata yake bi.
“Auren jinsi shine karshen barna, shine karshen rashin da’an da dan Adam zai aikata. Mu kuma a matsayinmu na masu kare hakkin dan Adam, a matsayinmu na afirika, ya saba komai namu. Addini, al’ada, zamantakewa. Ba ma mu ba ‘yan Afirika, ya saba zamantakewar dukkan dan’ Adam, shedanci ne kawai.
“Babu wani ‘yancin dan Adam da ya bada damar yin haka. Shedanci ne kawai suke yadawa a bayan kasa. Masana ilmin kimiyya da suka zurfafa, bincike, sun fahimci cewar bala’irar cutan Kanjamau ta samo asali ne saboda ma’abota luwadi da madigo, sune suka yada ta a duniya. Babu wata kyakyawar al’umma, mai tsarki da za ta yadda da wanzuwar ‘yan luwadi da madigo.
“Don haka mu ma kasashen Afirika, ba za mu taba ba bori kai ya hau ba. Dan haka muna yaba wa Shugaba Jonathan, saboda sama dokar fatattakar auren, jinsi da ya yi. Shugaba Jonathan ya ki amincewa wan nan barnar tasamu gindin zama a Nijeriya. A zama na da na yi a gidan kurkuku, na ga wadanda luwadi ya la’anta. Suka kare da cutar daji (mai suna cancer a yaren Turanci),” kamar yadda Sanatan ya bayyana a shekaru biyu da suka gabata.
Yayi wan nan hirar ne a ranar 19, ga watan Janairu, 2014. Da wata jarida mai suna NEWS DIARY, wacce ake buga ta a yanar gizo.
The post Sanata Shehu Sani ya bayyana akan auren jinsi ko auren dabbanci appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
