Hotuna: Kungiyar Izala ta ziyarci kasuwar Abubakar Rimi wanda ta kone
– A Laraba 30, ga watan Maris ne, kungiyar Izala ta jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Saleh Pakistan ta kai ziyarar jaje ga kasuwar Abubakar Rimi
– Akwai Dakta Pakistan, tare da tawagarsa sun kewaya cikin kasuwar da wuraren da abin ya faru domin ganewa idanunsu yadda lamarin ya kasance.
Rahotanni na nun cewa daga jaridar Rariya wanda, bayan nan ne shugaba Pakistan ya hadu da shugabannin kasuwar domin jajanta musu bisa faruwar wannan jarrabawa.
Shugaba Abdullahi Pakistan ya yi kira ga gwamnati akan ta dauki matakin taimakawa wadannan bayin Allah domin rage musu radadin abinda ya same su. Sannan yayi kira ga masu hannu da shuni akan su shigo su taimakawa yan kasuwar, domin ‘ya’yansu ne, kannensu ne kuma makwabtansu ne.
KU KARANTA KUMA: Abinda soji sun samu acikin akwatin gawa (Hotuna)
A cikin jawabin nasa, shugaban yayi kira ga yan kasuwar da su dauki wani mataki na tanadar kayayyakin kashe gobara da kansu, domin su dinga yiwa kansu taimakon gaggawa kafin a kawo musu dauki. Sannan ya ja hankalinsu da kalli wannan abu a matsayin qaddara, su mayar da lamarinsu ga Allah, su sani cewar wannan abu daga Allah yake kuma shine zai iya yaye shi garesu. Kuma daga karshe shugaba yayi musu dogayen addu’o’i akan Allah ya mayar musu da abinda suka rasa, kuma ya kiyaye faruwar hakan ana gaba.
Kungiyar Izala inda ta ziyarci wani kasuwar Sabon Gari
Su ma shugabannin kasuwar, sun nuna matukar jin dadinsu ga wannan ziyara da aka kawo musu da kuma addu’ar da akayi musu. Kuma sunce zasuyi amfani da nasihohin da shugaban kungiyar yayi musu insha Allahu.
In ba’a manta ba, tun acikin daren juma’ah ta wannan makon da muke ciki, kasuwar ta sabon gari ta kama da wuta, kuma sai da ta kai har yammacin Asabar ba a samu shawo kanta ba. Lamarin da ya jawo asarar dukiyoyin da ba za su lissafu ba, kuma ake hasashen wutar ta lashe shaguna da ba su gaza 3000 ba.
Kungiyar Izala ta Kano, kungiya ce da ta shahara da shiga lamarin al’ummar jihar, tana taya su murna akan dukkan abin alherin da ya same su, tana kuma tashi ta je ta jajanta musu idan wani abin jaje ya kama.
A kwanankin bayan can da jimawa, kungiyar ta kai ziyarar jaje ga yan kasuwar ‘Farm Center’ a lokacin da bam ya tashi a kasuwar, haka nan, akwanakin baya kungiyar ta kai ziyarar jaje bisa gobara da ta faru a kasuwar Singa. Irin wadannan ziyarori ba za su lissafu ba.
Yace wanda, “muna rokon Allah ya mayar wa da ‘yan kasuwar mu abinda suka rasa, ya ba su ladan wannan jartabawa, kuma ya kara daukaka wannnan kungiya tamu mai albarka.
Acikin kasuwar
Acikin kasuwa wanda wuta ta cinye
Inda yake tattauna da yan jarida
The post Hotuna: Kungiyar Izala ta ziyarci kasuwar Abubakar Rimi wanda ta kone appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.