Shugaba Muhammadu Buhari ya isa kasar Amurka
Shugaban kasa muhammadu Buhari ya isa Washington DC, kasar Amurka domin ya halarci taron makamashin Nuclear aranar 31 ga watan Maris.
Shugaban kasan wanda za yayi kimanin mako guda zaya halarci taron.
KU KARANTA: Garba Shehu Ya nemi PDP da ta bashi hakuri
Shugaba Najeriya yayin da yake sauka
Tawagar Amurka na tarbar shi
Daga dama, shugaban hukumar NIA, Abike Debiri, Ministan Ilimi, Ministan tsaro
Wannan shine karon shugaba Buhari na 2 da zuwan shi kasar Amurka tun bayan daya hau mulkin Najeriya. Shugaban kasar ya kuma ziyarci kasashe daban daban kamar su, Saudiyya, Faransa, Qatar, Misra, Ghana, Afirika ta Kudu, Ethopia, Ingila, Niger, Kamaru, CAR, India da Chadi.
Idan za’a iya tunawa, shugaba Buhari ya bayyana cewa tafiye tafiyen da yaye yi suna da amfani domin kuwa yana cigaba da kokarin maido da kudaden Najeriya wadanda aka sace ne. Tuni Kasar UAE ta sha alwashin maido da wasu makuden kudade da aka sace daca tarayyar Najeriya.
A wani labarin kuma, shugaba Buhari ya nemi yan najeriya da su kara hakuri da gwamnatin shi. Ya sha alwashin yin bakin kokarin shi domin ganin cewa an kawo canji da alayi ma al’umma alkari a lokacin yakin neman zabe daya gabata a shekarar 2015.
The post Shugaba Muhammadu Buhari ya isa kasar Amurka appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.