Akwai yiyuwar wanda tsohon gwamnan jihar Sokoto zaya koma jam’iyyar APC
– Akwai babbar alamomi wanda wani tsohon gwamnan jihar Sokoto mai suna Alhaji Attahiru Bafarawa zai koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC)
– Attahiru Bafarawa shine gwamnan Sokoto daga 1999 zuwa 2007 a karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) kafin ya koma Peoples Democratic Party (PDP)
Wani dan jaridar mai suna Umar Bandi Kofar Kware ya kawo labari wanda, wani tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar rusashiyar jam’iyyar DPP, Alh Attahiru Dalhatu Bafarawa, wanda ya yi taro da magoya bayansa domin bayyana musu maganar korar da aka yi masa daga jam’iyyar PDP, akan cewa ana yi mata kallon ta wasa ta wuce wasa domin wasu manya a jihar suka shigo ciki, ya kara da cewa shi zai bar siyasa baki daya, amma me sukace, suka bayyana masa cewa su koma jam’iyyar APC.
KU KARANTA KUMA: Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa na ce
Saidai wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta, ta fadi ce Bafarawa ya bayyana wa magoya bayan nasa cewa su ba shi kwana uku, zai bayyana musu matsayarsa akan komawa jam’iyyar.
Attahiru Bafarawa
Masu fashin bakin siyasar jihar, suna hasashen cewa, Bafarawa yana tunanin ta hannun da zai shiga jam’iyyar, da yadda zai kasance a karkashin tsohon yaronsa, Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda a dililin baya son zama jam’iyya daya da Wamakko, ya fice daga jam’iyyar, wanda yana daya daga cikin wadanda suka kaikomo wajen hadakan jam’iyyu da aka samar da hadakar da ta samar da APC, amma a dalilin yana jayayya da Wamakko, ya fice data cikin wannan tafiyar, da zimmar idan Goodluck Jonathan ya kai ga samun nasara, ya kauda Wamakko, lamarin da ake jin yana daya daga cikin ababen da suka ginawa Bafarawa manya da kananan matsaloli, a cewar majiyar, amma su magoyan suna tunanin idan Bafarawa yaki amincewa da komawa APC, yana yuwa zai koma sabuwar jam’iyyar PMP, wadda ba zamu amince mubi wannan sabuwar jam’iyyar ba, a cewar majiyar.
Sauya sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wata, a wajen Bafarawa ba wani sabon abu bane, domin shi dama bukatun kansa ne a gabansa, bana magoya bayansa ba, don haka duk inda yaga bashi zama babba, to ba zai amince ba, a cewar majiyar, amma a jira a gani mai zai fada zai koma APC, ko sai yakara ganin uwar bari, dashi da magoya bayansa, masu ra’ayi irin nasa, shi da hadiyar kudade kana a suna gaba da kiyayya da jama’a, saboda bambancin siyasa.
The post Akwai yiyuwar wanda tsohon gwamnan jihar Sokoto zaya koma jam’iyyar APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.