Akwai yiyuwar a cire Gwamnan Babban Bankin Najeriya
– Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefele, na fuskantar matsai daga yan Najeriya akan miyasa ya dauki yan uwan yan siyasa aiki a asirce
– Lauyoyi 10 na kundin tsarin mulki sun kai shi kara
– Za’a fara shari’ar nan bada jimawa ba
Godwin Emefele, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, yana fuskantar tsigewa bayan da wasu lauyoyin kundin tsarin mulkin Najeriya guda 10 suka kai shi akara akan laifin daukar ma’aikata a boye da kuma rashawa.
KU KARANTA: Amurka ta gano inda Yan Matan Chibok suke
Emefele ya fuskanci Allah wadai daga yan Najeriya bayan da rahotan ya bulla cewa ya dauki ya’ayan manya aiki wanda daga cikin su akwai diyar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, da kuma wasu ya uwan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wasu na ganin cewa ya dauki ya’ayan manyan aiki ne saboda ya kara samun kusanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ada ana ganin zaya cire shi.
Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa a cikin wadanda aka sanya sunayen su cikin masu kariya hadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma hukumar EFCC.
Wadanda suka kai karar sun roki kotu data Tilasta korar Emefele daga aikin shi akan rashawar daya aikata a cikin aikin shi.
A ranar 3 ga watan Mayu ake sa ran za’a fara shari’ar.
A wani labarain kuma, darajar Naira na cigaba da kara dawowa inda yanzu Dala 1 take a matsayin Naira 319. Wannan yao ne bayan da Dala 1 ta kai har darajar Naira 500 a cikin watan Fabrairu.
The post Akwai yiyuwar a cire Gwamnan Babban Bankin Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
