Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba 20 ga watan Afrillu, ku duba domin ku samu wadannan labaran.
1. Masu zanga zanga sunje gidan Obasanjo
Wasu masu zanga zanga sunje gidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo inda suke bayyana koken su akan gyaran iyaka da za’ayi a tsakanin kananan hukumomin Sango da Ijoko.
KU KARANTA: Amurka ta gano inda Yan Matan Chibok suke
2. Shugaban majalisar Dattawa ya sake gurfana gaban kotun CCT
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya sake gurfana a gaban kotun CCT inda a wannan karen Sanatoci 4 ne kawai suka rako shi.
3. An saki tankokin Mai 1194
Kamcfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya bayyana cewa ya saki tankoki dauke da mai 1194 zuwa fadin Tarayyar Najeriya
4. Osinbajo ya bayyana cewa baiyi murabus ba
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa baiyi murabus daga matsayin shi na Fasto ba daga cocin RCCG.
5. Shugaba Buhari ya amince da fara hada kasafin kudi na shekarar 2017
Cikin manyan abubuwan da aka tattaunwa a ya, shugaban kasa Muhammadu ya amince da fara hada kasafin kudi na shekarar 2017 inda hakan ya gudana a taron Zauren tsaro na kasa, a yau, a fadar shugaban kasa.
6. Amurka ta gano wurin yan matan Chibok
Kasar Amurka ta bayyana cewa ta gano inda yan Boko Haram suke cigaba da tsare wasu daga cikin yan Matan chibok.
7. Jihohi Bakwai ne kawa za’a iya ba btallafin N5000 a wata
Bincike ya nuna jihohi gu 7 ne kawai suka tantance yawan maasan da basu aiki a jihar da kuma iyakan yawan su. Jihohin sune; Bauchi, Cross Rivers, Ekiti, Kogi, Kwara Nija, Osun da Oyo.
8. Gwamnatin Tarayya zata fara biyan ma’aikata albashina a ranar 25 ga kowanne wata
Babban Akwaun Najeriya ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta shirya data ringa biyan ma’aikatan ta albashi a ranar 25 ga kowanne wata.
9. Ana zargin Fulani da sace da aikata manyan laifuka
Ana zargin Fulani da aikata manyan laifukka a jihar Benue, wadanda suka hada da sace wani Dan Sanda da kuma musayar wuta da sojojin Najeriya a Agatu.
10. Boko Haram ta kashe mutane 30
Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane kimanin 30 a garin Gulani inda ta sanya ma garin wuta ya kone.
The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.