An yabawa Buhari saboda cire tallafin man fetur, domin shi ne mafita rashin mai
Sammani Umar Gwammaja wanda yake zauna a garin Gwammaja dake jihar Kano ya rubuto dogon bayani wanda cire tallafin man fetur shi ne mafita. Saboda haka, farashin man fetur litar guda ta kara.
Tun daga jiya, Laraba, 11 ga watan Mayu, aka fara cece-ku-ce, dangane da sanarwar janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, wanda aka fi sani da subsidy. Karamin Ministan Albarkatun man fetur, Dakta Ibe Kachikwu ne da kan sa ya bayyana haka jim kadan bayan kammala wani taron masu ruwa da tsakin harkar mai da suka gudanar tare da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo a fadar shugaban kasa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Dalilin janye tallafin, za a rika sayar da litar man fetur Naira 145, sabanin yadda ake sayarwa N86 a yanzu.
Dakta Ibe Kachikwu ya bayyana cewa dalilan da suka haifar dajanye tallafin, sun kunshi yadda manyar dillalan mai ke kasa samun canji dalar Amurka wacce ta yi tashin-gwauron-zabi, kuma ta yi karanci a kasuwar musayar kudi a kasar nan. Wannan ya sa dilllalan kasa wadatar da ko da kashi 50 na fetur din da jama’ar kasar nan ya kamata su yi amfani da shi.
‘‘Bayan mun zauna taron tantance gaskiyar lamari, mun baje komai a faifai, sannan muka ce hanya daya da za a iya wadatar da mai ita ce a bai wa kowa damar shigo da shi a kan wani kayyadajjen farashi wanda shi ne mafita. Sai dai jama’a su kara hakuri, domin wadannan matsaloli duk gadar su muka yi daga gwamnatin da ta gabata.’’ Inji Minista Kachikwu.
KU KARANTA KUMA: Wani mutum ba zai ci abinci saboda kara farashin man fetur
Ganin haka ne ya sa na ce ya kamata na bayyana fahimta ta dangane da wannan matsala. Na farko dai ita kanta Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Kasa, NNPC ba ta iya samun yawan adadin makudan daloli da take bukata domin shigo da tataccen mai wanda zai wadaci cikin kasar nan.
Hikimar yin haka ita ce a bai wa manyan dillalan mai damar nemo kudaden kasashen waje da kansu, kuma su yi amfani da kudin su sayo fetur din su kawo su sayar. Hukumar NNPC ta ce a kullum ana shan litar man fetur milyan arba’in a kasar nan. Ashe kuwa aikin ba karami ba ne.
Shi ya sa ganin yadda gwamnati ke asara kuma man ba wadata yake ba, aka yanke shawarar sakar wa kowa mara ya shigo da mai kuma ya sayar, domin fetur abu ne da ba ya kwantai. Hakan kuma zai kawo karshen yadda kananan masu saida fetur ke ta boye shi su na saidawa da tsadar bala’i.
Matukar mai ya wadata, to za a kawo karshen bumburutu inda za ka ga matasa majiya karfi maza da mata sun mika rayuwar su ga sayar da fetur a cikin jarkoki da galan-galan maimakon su samu sana’o’in dogaro da kai. Tuni dai dama masu tunanin cewa fetur albarkatun kasar mu ne da Allah ya albarkace mu da shi, don haka sai mu sha shi kyauta ko kasa da kasashe masu tasowa, wannan tunanin nasu ya kau, domin kowa yanzu ya san irin makudan kudaden da ake kashewa wajen hako shi da kuma tace shi, ya nunka kudin da ake sayar da shi a gidajen mai.
Daga cikin gidajen mai 26,700 da muke das u, 37 ne kacal mallakar Gwamnati, wato NNPC Mega Stations da aka yi a kowace jihad a Abuja. Sai guda 2453 mallakar manyan dillalan mai wato Major Marketers, irin su Total, Mobil, Oando, Conoil, Forte Oil da MRS. Dukkan saura sama da 24,226 duk na kananan ‘yan kasuwa ne, wato Independent Marketers, da aka fi sani a kungiyance da suna IPMAN.
An taba yin wani lokaci nan baya ba da dadewa ba, inda kusan kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin kasar nan duk ya na tafiya ne wajen biyan tallafin mai ga manyan masu safarar fetur. Abin da gwamnatin Buhari ta yi shi ne dattako, kuma iya tafiyar da shugabanci ne. Wadannan kudaden fetur idan an tara su, aiki ne za a yi wa jama’a, ba masu wawura ne za su wawure su kamar irin yadda ya faru a gwamnatin baya ba. Cikin kankanen lokaci za a ga irin alherin da ke tattare da janye wannan tallafi.
Bugu da kari kuma kudaden da gwamnatin tarayya ke bai wa jihohi da kananan hukumomi zai karu ainun daga dan abin da a yanzu ake tsakura musu. Ashe kenan ya zama wajibi ga al’umma su tashi tsaye su rika zuba ido kan kudaden da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomin su za su rika yi musu aiki da su. Wannan gwamnatin yi wa talakawa aiki ce ba gwamnatin tarawa da kwashewa ba ce.
Ni a nawa tunanin, Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ce ma ya kamata ta fito ta nuna alfanun cire tallafin mai, domin ta na sane da irin asarar da gwamnati ke yi wajen kwasar bilyoyin kudin da ya kamata a yi wa jama’a aiki, ana biyan dillalan mai da sunan tallaffin mai. A cikin shekra daya kacal za a iya tara makudan kudaden da za a yi ayyukan inganta rayuwa wanda zai amfanini daukacin al’ummar kasar nan baki daya.
Ba wai tilas farashin a N145 zai tsaya ba, gwamnati za ta rika saida nata kasa da haka, su kuma ‘yan kasuwa ne za su saida a N145. Hikimar dai da farko ita ce a wadata mai. Sai kuma su ‘yan kasuwar mai tilas hakan zai sa su shiga taitayin su. Tunda mai dai zai wadata, to kun ga kenan duk wanda ya tsula kudi, ba za a saya ba, sai a guje shi, a bar shi ya yi ta tsula asara.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari gwamnati ce mai niyyar yi wa jama’a aiki tukuru. Kasafin kudin bana ya tabbatar da alherin da ke tattare da wannan gwamnati, sannan kuwa a halin yanzu hakan bai hana Hukumar NNPC ci gaba da kokarin ganin ta inganta matatun kasar nan ba.
The post An yabawa Buhari saboda cire tallafin man fetur, domin shi ne mafita rashin mai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).