Shigowar yanzu: Bam ya tashi a ofishin gwamnati dake Maiduguri
– Bam ya fashe a ofishin Gwamnati dake Maiduguri, wani babban birnin jihar Borno
– A sakamakon haka, kimanin mutane guda hudu sun rasa rayukansu
Wani gawan dan kunar bakin wake
Bayanai da suka iso kunnen NAIJ.com sun nuna cewa bam din ya tashi ne a ofishin gwamnati dake Maiduguri a jihar Borno. Izuwa wannan lokaci, an tabbatar da cewa mutum guda hudu sun rasa rayukansu.
KU KARANTA WANNAN: Dan kunar bakin wake ya tashi bam a Maiduguri
Duk da ba’a samu cikakkun bayanai a kan al’amarin ba, akwai kishi kishin cewa mutane da dama sun jikkata, kamar yanda aka gani a shafukan twitter na mutanen na Maiduguri.
Tun dai sojojin JTF da na farar hula sun mamaye gurin da wannan al’amari da ya faru. Mai karatu kar ya manta a jiya ne kawai wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani Masallaci da ke maiduguri inda a nan ma mutum guda shida suka rasa rayukansu.
The post Shigowar yanzu: Bam ya tashi a ofishin gwamnati dake Maiduguri appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).