Buhari ci abincin safe da shugabannin duniya kafin taron yaki da rashawa (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci abincin safe da wasu shugabannin duniya a gidan Lancaster dake garin Landan, wani babban birnin kasar Ingila, kafin ya halarci a taron yaki da rashawa a yau, Alhamis, 12 ga watan Mayu
Wani Ministan kasar Biritaniya a mukamin akan ayyukan kasashen waje a karkashin kasar Ingila mai suna Hugo Swire, shine maraba Shugaba Buhari da sauran ma’aikata kafin taron yaki da rashawa
KU KARANTA KUMA: Buhari ya maganta a taron yaki da rashawa a Landan
Shugaba Buhari kuma ya ci abincin safe da shugabannin kasashen duniya a gidan Lancaster, inda wani Babban Sakataren kasar Amurka akan kasashen waje mai suna John Kerry ya halarci. Kuma, wata Manajin Daraktar International Monetary Fund (IMF), mai suna Christine Lagarde da shugaban kasar Afghanistan mai suna Ashraf Ghani suka halarta.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake amsa tambayoyi daga yar jaridar CNN a garin Landan
Shugaba Buhari da wani ma’aikacin gwamnatin kasar Biritaniya mai suna Hugo Swire
Inda aka maraba Shugaba Buhari zuwa Landan
Shugaban kasar Najeriya da wasu shugabannin duniya a lokacin abincin safe
Shugaba Buhari ya zauna a tsakanin Christine Lagarde, wata Manajin Daraktar IMF da wani Babban Sakataren kasar Britaniya akan harkokin kasashen waje
The post Buhari ci abincin safe da shugabannin duniya kafin taron yaki da rashawa (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).