IPOB ta kai Buhari kara, tana neman a bata Biliyan 8.5
– Kotu zata fara sauraron kara akan gwamnatin Najeriya a watan June
– Kungiyar IPOB ta kai karar domin tana so a bata Naira Biliyan 8.5 saboda mutanen ta da aka kashe, raunata a lokacin zanga-zanga
Mambobin kungiyar IPOB a lokacin da suke zanga zanga
Babbar kotun gwamnatin Tarayya dake a garin Abuja zata fara sauraron wata kara akan gwamnatin tarayya a ranar 21 ga watan Yuni na 2016.
Kungiyar IPOB ta nemi a bata kudaden saboda biyan mambobin ta wadanda jami’an DSS suka kashe da wadanda hukumar ta raunata a yayin da ake gabatar da zanga-zangar.
A cewar jami’i mai hudda da jama’a na kungiyar, kimanin mutanen kungiyar 153 ne aka kashe a Onithsa da Aba da sauran wuraren da aka gudanar da zanga-zanga.
Ta kuma bayyana cewa an yima kimanin 50 aiki bayan da suka samu raunuka daban-daban. Kungiyar kuma ta nemi a saki shugaban ta kuma Daraktan Rediyon Biafra, Nnamdi Kanu.
Shugaban kungiyar na zargin shugaban kasa `muhammadu Buhari da cigaba da rike shi da kuma hana bada shi Beli kamar yadda kotu ta bada umurni.
Nnamdi kanu dai yana can tsare a cikin gidan kurkuku tunda aka kama shi a ranar 14 ga watan Aktoba na shekarar 2015.
A wata fira da yan Jarida sukayi da shugaban kasa `muhammadu `buhari a ranar 31 ga watan Disamba, shugaba Buhari ya bayyana cewa Nnamdi Kanu ya aikata babban laifi akan Najeriya domin ya shigo da makamai kuma yana rike da takardar shaidar zaman dan kasa na kashe guda 2 dan haka ba za’a sake shi ba.
Kimanin sama da watanni 5 ke nan yan kungiyar IPOB nata zanga-zanga a jihohin daban daban a Najeriya, musamman jihohin kudu maso yamacin Najeriya.
A wani labarin kuma, sojojin Najeriya sun bayyana cewa sun kama shugaban kungiyar Niger Delta Avengers a can yankin kudu maso kudancin Najeriya. Kimanin wata 1 ke nan da fitowar kungiyar inda ta ringa fasa bututun mai tana aiwatar da ta’addanci da asara mai girma akan Gwamnati da kuma al’ummar Tarayyar Najeriya.
The post IPOB ta kai Buhari kara, tana neman a bata Biliyan 8.5 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).