– Hukumar hana almundahana da kudaden al’umma (EFCC), ta matsa lamba akan bincike ga Gwamnatin Aregbesola na Jihar Osun
– Binciken yazo ne bayan da wasu kungiyoyi sukayi rubuta akan cewa yana al’mundahana da kudaden kananen hukumomi
Rauf Aregbesola
Akwai alamu cewa Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola na fuskantar matsi bayan da hukumar EFCC ta kara matsa lamba akan Gwamnatin tashi a cigaba da bincike kan rashawa kudaden kananen hukumomi da akeyi a cikin jihar.
Shugaban hukumar EFCC dake Ibadan, Akaninyene Ezima ne ya gayyaci yan kungiyar Civil Societies Coalition For the Emancipation of Osun state.
Takardar daya aika masu da ita aka rubuta ” Wannan domin sanar daku cewa mun karbi takardar koken ku wadda kuka aiko a ranar 4 ga watan April wdda kuayi ma take da rahoton canza kudaden kananen hukumomi 30 na jihar Osun.
Wasu yan kungiyoyi sun zargi Gwamnan Jihar Rauf Adesoji Aregbesola da boye udaden kananen hukumomin a wata takarda da suka aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Takardar yan kungiyar tace ” Wannan domin kara tabbatar da cewa Gwamna Rauf Aregbesola ya dakatar da duka wasu ginshikai na Damakaradiyya a Jihar Osun wanda kuma hakan bai kamata ba kuma bash da hurumin da zayayi hakan. Ya nada Daraktoci masu mataki na 14 domin hakan ya bashi dama ya boye kudaden kananen hukumomin yadda yake so. Hakan ya saba ma Sakin layi na 7 na 1 na kundun tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999.
“Ya kamata gwamnatin Tarayya, Majalisar Jihar, da kuma hukumomi masu yaki da rashawa su binciki yadda Aregbesola yake yima kananen hukumomi titi ba atre da bin ka’idojin public Procurement Act ba.
” Abubuwan da yake yi suna jaza wahala da tsananin matsi ga ma’aikata, mutane da kuma wadanda sukayi Ritaya daga aikin gwamnati a cikin Jihar
Gwamna Rauf Aregbesola yana daga cikin manyan masu sukar gwamnatin Jonathan a wancan lokaci inda suke zargin ta da rashawa da al’mundahana.
Сотрудница подразделения столичного главка Росгвардии завоевала «золото» на чемпионате войск по легкоатлетическому кроссу
Чемпионат по военно-спортивному многоборью среди росгвардейцев завершился в Грозном
Чемпионат по военно-спортивному многоборью среди росгвардейцев завершился в Грозном
В День парашютиста героем рубрики «Знай наших» стал сотрудник вневедомственной охраны столичного главка Росгвардии младший лейтенант полиции Александр С.