Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin 16 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu wadannan manyan labaran.
1. Shugaban kasa Buhari zaya ba yan Najeriya N5000
Kimanin mutane Miliyan Daya mafi fama da talauci a Najeriya zasu amfana daga shirin shugaban kasa muhammadu Buhari naba N5000 a kowanne wata.
2. Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin kungiyoyin Kwadago domin a tattauna
A cigaba da shirin da yan kungiyar kwadago sukeyi domin su kulle Najeriya kamar yadda sukayi bayani, gwamnatin Tarayya ta gayyace su zuwa tattaunawa.
3. Shugaban kasar Amurka na shirin zuwa Najeriya.
Barack Obama na kasar Amurka na shirin zuwa Najeriya domin tattaunawa akan yaki da Boko Haram da kuma lamurran da suka shafi kasashen guda 2.
4. Fasto Adeboye ya maganta akan Najeriya
Fitattacen Malamin nan na addinin Kiristanci ya maganta akn wasu lamurran da suka shafi najeiya. Fasto Adeboye yana cikin manyan malaman Kirista a najeriya
5. Anga wani Maye na yawo akan iska a Calabar
Anga wani wanda ake zargin cewa Maye ne yana yawo a saman iska a Calabar.
6. Yan majalisa na PDP sun hana kachikwu shigowa majalisa
Yayin da majalisa ta kira shi domin a tattauna, wasu yan majalisar PDP sun nemi su hana Ministan Mai shiga. Ministan yana daga cikin manyan masu fitowa a jarida a yanzu
7. Wani mutum ya mutu a kasar Thailand bayan ya sadu da mata Maza
Wani mutum ya rasa ransa a kasar Thailand bayan da ya sadu da wata mata Maza.
8. Hukumar EFCC na shirin gayyatar Jonathan
Hukumar EFCC na shirin gayyatar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
9. Abunda karamin Ministan Mai ya fada ma Yan majalisa
Bayan daya amsa gayyatar su, Minstan Mai ya fada ma yan majalisa abubuwa muhimmai guda 5. Wannan na daga cikin manyan abubuwan da ya sanar da yan majalisan
10. Shugaban kasa Buhari ya gana da tsohon Kwamandan sojojin Amurka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Wesley Clark a jiya
The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).