Ku karanta za’a yi a jihar Bauchi saboda janye tallafin man fetur (hotuna)
– An rahoto wanda za’a gudanar da zanga-zangar boyon bayan janye tallafin man fetur a jihar Bauchi
– Za’a gudanar da zanga zangar lumana a jihar Bauchi na goyon bayan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inji Shugaban Matasan jam’iyyar APC
Bashir Abdullahi El-Bash, ya bayyana wanda shugaban matasan jam’iyyar APC na jihar Bauchi Malam Nasiru Umar Gwallaga haka kuma daya daga cikin manya manyan magoya bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a jihar Bauchi yana kiran matasan garin Bauchi masu goyon bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da su fito domin nuna goyon bayan su ga wannan Gwamnati.
“Kasancewar wannan gwamnatin zuwan ta ta samu nasarori musamman harkar tsaro a wannan yanki na Arewa maso gabas. Don haka ya zama wajibi akan mu fito mu nuna ma wannan gwamnati goyon baya, kada mu sake wasu su yi amfani da wannan dama wurin kawo cikas ga wannan Gwamnati na canji da talakawan kasar mu muka yi.
KU KARANTA KUMA: Wani dan majalisar tarayya ya maganta kan siyasa
“Don haka kada mu sake wasu ‘yan hana ruwa gudu su yi amfani da wannan dama su kawo wa kasar mu koma baya daga gyaran kasa da yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnatin keyi.
“Ya zamar mana dole matasa mu kare Gwamnatin da mun yi imanin cewa ta zo ne domun cire kasar mu dama al’umma cikin mummunan yanayi na kuncin rayuwa. Don haka kada mu sake wasu masu amfani da wannan tallafin su yi amfani da ‘yan Kwadago domin su kushe Gwamnatin Buhari.
“Yanzu haka akwai mutane masu yawa a kasar nan dake adawa da gwamnatin Buhari saboda su ba masu gaskiya bane, domin Gwamnatin Buhari tana yaki ne da barayi.
“Shugaban Matasan jam’iyan APC na jihar Bauchi yana kira ga matasan musamman mazauna garin Bauchi cewa gobe Talata ne za’a gudanar da wannan babban taron nuna goyon bayan Mutanen Bauchi ga Gwamnatin Buhari.”
Inda Ahmadu Manager Bauchi, a madadin magoya bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saki wani takarda za’a Gudanar da babban taron a yau, Talata, 17 ga watan Mayu.
“Titin Kobi kusa da Asibitin Makka zuwa Kofar fadar Bauchi zuwa Titin Makera, zuwa titin Ahmadu Bello, zuwa Gidan Gwamnatin jihar Bauchi daga nan sai a dawo cikin gari domin gabatar da jawabai daga bakin Shugabannin Kungiyoyi da suka halarci wannan babban taron.
“Allah ya kai mu ya ba mu ikon halarta Amin. Allah kabawa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ikon sauke nauyin shugabanci akanta. Muna fatan Alkhairi ga wannan gwamnatin Shugaba Buhari Muhammadu.”
Yan kungiyar Kwadago kun makara har gobe mu talakawan Nijeriya muna tare da Gwamnatin Buhari. Domin mun yi imanin cewa wannan gwamnatin ba azzaluma ba ce.
The post Ku karanta za’a yi a jihar Bauchi saboda janye tallafin man fetur (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).