Abunda wani dan Boko Haram ya bayyana ma sojoji
– An kama wani dan Boko haram
– Ya bayyana cewa ya bar kungiyar da dadewa
– Ya bayyana cewa shiga kungiyar babu kawai
Wani dan kungiyar Boko haram da sojoji da yan kungiyar Civilina JTF suka kama ya bayyana cewa ya bar kungiyar tun shekara ta 2014.
duk da cewa Naij.com baza ta iya tantance ingancin Bidiyon ba saboda a shafin facebook aka saka shi, amma an nuna cewa dan kungiyar an kama shine bayan daya baro Legas zuwa garin su wajen matar shi a garin Bama.
Dan kungiyar ya bayyana cewa a shekarar 2012, shekaru 3 ke nan bayan da kungiyar ta fara ta’addanci ya shiga cikin kungiyar bayan da wani dan unguwar su mai suna Muhammad yayi mashi wa’azi. Ya bayyana cewa ada shi Malamin makarantar Firamare ne amma daya shiga kungiyar sai aka umurce shi daya kona makarantar amma yaki.
Ya bayyana cewa duk wanda ya bijire ma umurnin shugabannin kungiyar ana kashe shi dan haka ne ma bai nuna cewa fita za yayi ba.
Da aka tambaye shi ya bada sunayen mutanen daya sai yan kungiyar sai ya bada sunayen mutane 3 wanda kuma dukkanin su an kashe su tunda jimawa.
Wannan Bidiyon yazo ne bayan da a kwanakin baya yan kungiyar suka fitar da wani Bidiyo nasu wanda izuwa yanzu shine na karshe inda suka sha alwashin kai hari afadar shugaban kasa, sannan kuma suka bada gargadi ga shugaban kasa `muhammadu Bhari.
Sojojin Najeriya dai na cigaba da samun nasara akan yan kungiyar inda ahalin yanzu da yawa daga cikin yan kungiyar sun shiga buya ko kuma an kashe su.
A wani labarin kuma, Minsitan Tsaro na Najeriya , mannir Dan Ali, ya bayyana cewa da sannu sojojin Najeriya zasu ruguza kungiyar Boko haram. Ya bayyana hakan ne a kwanakin baya a lokacin daya je Jihar Zamfara domin ya duba wasu aiyuka da aykeyi a barikin sojoji dake a wurin. ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa `muhammadu `buhari zata kula da jin dadin jami’an tsaro yadda ya kamata.
The post Abunda wani dan Boko Haram ya bayyana ma sojoji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).