Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice ranar Talata
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata 17 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu wadannan manyan labaran.
1. Gwamnati ta saduda, ta kafa kwamiti duba yiyuwar rage farashin Mai
ayan da kungiyoyin kwadago suka sha alwashin tafiya yajin aiki, bayan kwanaki 2 ana tattaunawa da gwamnatin Najeriya, kungiyoyin sun sha alwashin tafiyar yajin aikin kamar yadda suka riga suka tsara.
2. Yan kuniyar Kwadagao sun bayyana cewa babu gudu babu ja da baya
Yan kungiyoyin kwadago sun bayyana cewa tafiya yajin aiki babu gudu babu ja da baya. Wannan yazo bayan da gwamnatin Tarayya ta kai su kara a kotu inda kotu ta umurce su da kada su tafi yajin aikin.
3. Gwamnatin Najeriya ta kai yan kungiyar kwadago kara kotu
Gwamnatin Najeriya ta hanyar Ministan shari’a kai yan kungiyar kwadago kara kotu inda ta nemi a hana su tafiya yajin aiki.
4. Yarabawa da Igbo sunyi fada a Mushin, Legas
Kabilar Yarrabawa da Igbo sunyi fada a Mushin dake Legas inda aka kona wani gida guda daya. Yar yanzu da ba’a yadda fadan ya kaya ba.
5. Balarabe Musa bai goyi bayan cire tallafin mai ba
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Balarabe Musa ya bayyana cewa bai goyi bayan cire tallafin Mai ba a Najeriya.
6. Kungyar Malamn jami’a bata goyi bayan cire tallafin Mai ba
farfesa Biodun Ogunyemi, shugaban kungiyar malam jami’o’in Najeriya ya bayyana cewa kungiyar bata goyi bayan cire tallafin Mai ba.
7. An gano wata rashawa a zauren gudanarwa na kasa
Rahotanni na nuna cewa Babban Akawun Najeriya ya damfari mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo.
8. Shugaban kasa `buhari zaya nemi taimakon Jonathan
Akwai alamun cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya nemi taimakon tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan akan sabbin kungiyar tsagerun Nija Delta.
9. Taron Gwamnati da kungiyar Kwadago; an tashi bawan-bawan
Kungiyoyin kwadago sun sha alwashin cigaba da gudanar da zanga-zanga akan karin farin Mai da gwamnatin tarayya tayi.
10. Abincin Mata mai kara kuzari
Akwai abinci mahimmai da mata ke ci domin ya kara masu zama mace.
The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice ranar Talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).