Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Май
2016

Kungiyar kwadago ta hakikance kan tafiya yajin aiki

0

– Kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana cewa yajin aiki babu gudu babu ja da baya

– Kungiyoyin sun fusata akan umurnin da kotu ta bada na kada a tafi yajin aiki bayan da Gwamnatin tarayya ta kai kungiyoyin karar

– Akwai yiyuwar kin halarta taron ganawa da Sakataren gwamnati

Yan kungiyar Kwadago

Kungiyoyin NLC da TUC na shirin shiga yajin aiki na gama garin kamar yadda suka shirya tun farko. A yau ne Talata, 17 ga watan Mayu na 2016 kungiyoyin guda 2 suka sake tattaunawa da marece inda suka sake jaddada cewa tafiya yajin aiki a tsakiyar daren yau babu gudu kuma babu ja da baya. Jaridar Vanguard ta ruwaito.

A yau ne wata kotu ta ba kungiyoyin umurni cewa kada su shiga yajin aikin, bayan da gwamnatin Najeriya ta kai kungiyoyin guda 2 kara a kotun.

A memakon su shirya bin umurnin kotu, an ga yan kungiyar ta kwadagon suna ta shirya meeting domin tabbatar da cewa sun tafi yajin aikin kamar yadda sukayi alkawari tun farko.

Wata majiya daga wuraren yan kungiyar ta bayyana cewa ” Muna nan akan batun mu domin tabbatar da cewa an tafi yajin aiki. karar da gwamnati ta kai ku kotun ma’aikata a yau ita ta kara harzuka mu ma.

Ana tsammanin yan kungiyar zasu bijire ma taron da zasuyi da gwamnati a yau da adre domin kuwa babban sakataren kungiyar ma’aikatan wutan lantarki ya bayyana cewa shi ba zaya shiga yajin aikin ba.

Naij.com zata cigaba da sanar daku yadda lamarin ya kaya

 

 

The post Kungiyar kwadago ta hakikance kan tafiya yajin aiki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса