Inda Najeriyan ke tunani yajin aiki, ku gano abinda soji yi da Fulani makiyaya (hotuna)
– Dakarun sojojin kasar Najeriya sun cafke yan fashi guda biyu
– Soji kuma sun kama babura da yawa
– Rudunar soji sun samu nasara inda sun hallaka wurin masu rushewa a Arewa maso gabashin kasar a jiya, Talata, 17 ga watan Mayu
A kimanin sati guda da ya wuce ne, dakarun sojojin Najeriya sun samu wani sabon nasara da wasu yan kungiyar Boko Haram da barayin dabbobin da masu satar shanu da wasu yan fashi, wadanda sun kai hari akan jihar Zamfara.
KU KARANTA KUMA: An kakkabe sansanin Boko Haram a dajin Sambisa
Dakarun sojojin kasar Najeriya suke ci gaba da murkushe halin ta’addanci a kasar, kamar yadda sun kakkabe sansanin wadanda aka zargin barayin shanu a jihar Zamfara.
Guda biyu acikin masu satar shanu wadanda dakarun sojoji sun cafke bayan sun kakkabe sansanin barayin shanu
Wanna lamarin take aukuwa, inda kungiyoyin kwadagon dake Najeriya a karkaskin Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC), suke son shiga yajin aiki a yau, Laraba, 18 ga watan Mayu.
A takarda wanda kakakin rundunar hukumar soji mai suna Kanal Sani Kukasheka Usman ya aiki am yan jaridu a Laraba, 18 ga watan Mayu, take nuna cewa wanda, “A Talata, 17 ga watan Mayu, 2016 dakarun sojoji daga Birigadin sojin Najeriya, wadanda suke yi aiki a karkashin sunan Operation MESAa jihar Zamfara, sun kai wadanda aka zargin barayin shanu da yan fashi masu bindigogi hari a dajin Yan Mangu, kusa da kauyen Dandindin, da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
“Rundunar sojojin sun kama yan fashi guda biyu, inda sun samu bindigogi daban-daban kamar AK-47 da bindigogi guda uku da babur guda daya.
“Sojin sun cafke masu tuhuma guda biyu inda suka tsere daga sansaninsu. Amma, dakarun sojojin sun kakkabe sansanin barayin shanu gaba daya a wurin, inda sojin sun samu nasara can.”
Ga sauran hotuna a kasa:
Rundunar soji sun kona wani babur da wuta bayan sun kakkabe sansanin wadanda aka zargin yan fashi
Anan, akwai bindigogi guda hudu ne harsasai wadanda soji sun kama daga barayin dabobbi a jihar Zamfara
The post Inda Najeriyan ke tunani yajin aiki, ku gano abinda soji yi da Fulani makiyaya (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).