Ku gano abinda rundunar soji yi da sansanin Boko Haram guda biyu a dajin Sambisa (hotuna)
– Dakarun sojojin kasar Najeriya suke bukata yabawa daga al’ummar Najeriya gaba daya
– A Talata, 17 ga watan Mayu ne rundunar sojin Najeriya sun kai sansanin Boko haram guda biyu hari dake dajin Sambisa
Rahotanni na nuna cewa wanda sojoji sun kakkabe Sansanin yan ta’addan Boko Haram guda biyu.
Wani labari ta ci gaba cewa wanda, a jiya Talata, 17 ga watan Mayu ne dakarun sojojin Nijeriya suka yi nasarar kakkabe sansanin yan Boko Haram dake Njimia dake a tsankakanin dajin Sambisa da kuma kauyen Alafa, dake Arewa maso gabashin Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Ga wani dan Boko Haram wanda sun kama a jihar Borno
A yayin artabu da ‘yan Boko Haram din a kauyen na Alafa, sojojin sun yi nasarar kashe sha biyar daga cikin yan bindigan, sannan kuma sun ceto mutane 40 da ‘yan bindigan suka sace, wadanda akasarin su yara ne da mata.
Haka kuma sun kwace makamai da dama a hannun yan bindigan. Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin wanijami’i mai hudda da jama’ar rundunar sojojin mai suna Kanal Sani Kukasheka Usman.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a wani labari a kwanaki biyu da suka wuce wanda wata kungiya masu hallakan sun samu makamansu daga makaman wadanda sun sata acikin ma’ajiyar makaman hukumar sojin Najeriya.
Ga hotunan a kasa:
Dakarun sojoji guda biyu da tutar yan kungiyar Boko Haram bayan sun kakkabe sansanin Boko Haram a dajin Sambisa dake Arewacin kasar
An kone sansanin yan ta’addan Boko Haram
Wasu dakarun sojojin Najeriya a cikin jiragen samar sojin
Wasu babura wadanda an kama daga yan kungiyar Boko Haram
Inda rundunar sojin Najeriya suka kakkabe sansanin yan ta’addan Boko Haram da ke dajin Sambisa a Arewa maso gabashin Najeriya
Wata motar yan Boko Haram wanda sojin sun kama
Anan akwai mata da yara wadanda dakarun sojin sun ceto, suna cikin mutane wadanda an garkuwa da su
Wani gawan dan Boko Haram bayan an kashe shi
Anan kuma, akwai gawan wani dan kungiyar Boko acikin dajin Sambisa
Dakarun sojoji sun kone wasu babura da motar yan ta’addan bayasun kama su
The post Ku gano abinda rundunar soji yi da sansanin Boko Haram guda biyu a dajin Sambisa (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).