Manyan labaran da sukayi fice a ranar Laraba
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba 18 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu wadannan manyan labaran.
1. Kungiyar Kwadago ta fara zanga zanga
A jiya ne kungiyar kwadagon Najeriya ta fara zanga-zanga inda ta sha alwashin cigaba da gudanar da yajin aikin har san gwamnatin Tarayyar Najeriya ta maido da tallafin Mai data cire a makon daya wuce.
2. An cigaba da shari’ar Saraki
A jiya ne aka cigaba da Shari’ar Bukola saraki a kotun CCT inda ake cigaba da tugumar shi akan laifin kin bayyana kaddarorin shi a lokacin da yake Gwamna a Kwara a 2003.
3. Tsageranci a Nija Delta
Kungiyar Egbesu water Lions ta Nija Delta ta sha alwashin hada hannu da Niger Delta Avengers domin tabbatar da cewa babu mai daya fita yanki har sai an biya masu bukatun su.
4. An gano daya daga cikin yan Matan Chibok da Boko haram ta sace
An gano Amina Ali Nkek, daya daga cikin Yan matan Chibok da Boko Haram ta sace a watan Afrilla na shekarar 2014 a makarantar kwana dake a jihar Borno.
5. Wanda yayi tattaki domin Buhari ya bayyana cewa bai gamsu da mulkin Buhari ba
Hashim Suleiman, mutumin da yayi tattaki daga Legas zuwa Abuja domin rantsar da shugaban kasa `muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai gamsu da shekara 1 da Buhari yayi ba akan mulki.
6. Kotun yammacin Afirika na neman amsa daga Gwamnatin Najeriya
Kotun yankin yammacin Afirika na neman gwamnatin najeriya ta bata amsa akan cigaba da tsare Sambo Dasuki da take yi.
7. Kungiyar Kwadago ta bayyana shirin ta
Kungiyar Kwadago a jiya Abuja ta bayyana cewa tana godiya ga mambobin ta wadanda suka fito yajin aiki inda ta bayyana cewa za’a cigaba da yajin aikin.
8. Shugaba Buhari ya jagoranci taron Zauren Kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zauren gudanarwa na najeriya a jiya 18 ga watan Mayu.
9. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori shugaban Immigration
A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar Immigration, Martin Abeeshi daga bakin aikin shi.
10. Sojojin Najeriya sun ruguza sansanin manyan barayin Shanu a Zamfara
Sojojin Najeriya sun ruguza sansanin manyan barayin shanu a jihar Zamfara.
The post Manyan labaran da sukayi fice a ranar Laraba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).