Yajin aiki: Ku karanta dalilai guda 8 matalauta suke so cire tallafin man fetur
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda hukumar man fetur ta sanad da karin kudin mai a sati da ya wuce
– A Laraba, 18 ga watan Mayu ne wasu membobin kungiyar kwadago sun fita saboda zanga-zangar kan cire tallafin man fetur
– Yan kungiyar Nigeria Labour Congress suke rabuwa kan yajin aikin jiya a kasar
Wani dan jarida mai suna El-Bash ya kawo rahot wanda, talakawan Najeriya sun ki yarda da zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kira a dalilin cire tallafin mai saboda sun fahimci:
1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba yarda da abunda zai cutar da kasa da ‘yan kasa ba.
2. Mummunan cin hancin da wasu tsuraru ke yi a harkar tallafin.
3. Faduwar naira ne da lalacewar tattalin arzikin da gwamnatin da ta gabata ta haifar ya jawo wannan kari.
KU KARANTA KUMA: An hana kungiyoyin kwadago da shiga yajin aiki
4. Man fetur din da Nijeriya ta dogara da shi ya fadi warwasa kasuwar duniya.
5. Akwai masu kokarin bata duk wani ci gaba saboda manufa ta siyasa.
Zanga-zangar kan cire tallafin man fetur
6. Ba wani canjin da ya taba faruwa a duniya a cikin jindadi.
7. Kwashe kudin kasa zuwa wasu kasashen duniya da marasa tausayi suka yi shi yakara jefa jama’a cikin ni ‘ya su.
8. Miliyoyin da ake kashewa wurin yakar Boko Haram da aka bari ta yi karfi a da, ya jawo matsala ga tattalin arzikin kasa.
Kari da haka mu talakkawa mun fahimci kasashe da yawa kamar Saudiyya, Kuwait da Binizwela sun yi wannan kari kuma ba mu ji an yi zanga- zanga ba saboda fahimtar talakawansu game da abunda ke faruwa.
Don haka ba wanda ya isa ya maida hannun agogo baya, talaka ya gane. Saka rigar NLC ba zai hana a ci gaba da binciko barayi ba. komai tsanani akwai sauki tare da shi. Talakka zai yi ta hakuri har sai ya ga Najeriya ta ci gaba.
The post Yajin aiki: Ku karanta dalilai guda 8 matalauta suke so cire tallafin man fetur appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).