Zamu kulle duka hanyoyin satar Mai – Buhari
– Shugaban kasa `muhammadu Buhari ya bayyana cewa zaya kulle duka hanyoyin satar Mai
– Shugaban kasar ya fadi hakanne a lokacin da yake a Landan inda yayi wata fira da BBC Hausa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi fira da gidan Rediyo na BBC Hausa a yayin da yake ziyarar kasar Ingila. Shugaban kasar ya bayyana cewa nan da shekaru 2 Najeriya zata cigaba sosai kuma zata fi yadda take a yanzu.
KU KARANTA: Kungiyar Kwadago ta shirya cigaba da yajin aiki
Shugaban kasar ya bayyana cewa ada, a lokacin da yake Ministan Mai a 1976, shine ya fara gina Matatun Mai na farko na Najeriya wanda har a yanzu ba’a sake gina wasu ba. Ya bayyana cewa A halin yanzu Aliko Dangote yana gida wata Matatar mai wadda keda karfin tace Durom din mai 650,000 a kowacce rana.
Ya bayyana cewa zaya kulle duka wasu hanyoyin da ake satar Mai.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai shine Ministan Mai a Najeriya. Ya nada kanshi ne a watan Satumba daya wuce inda ya bayyana cewa shi zaya jagoranci ma’aikatar. Sannan daga baya ya nada Ibe kachikwu a matsayin karamin Ministan Mai.
Kasar Najeriya dai itace kasa wadda tafi kowacce albarkatun Mai a Nahiyar Afirika. A shekarun baya, a kulluma ana fitar da Durum Miliyan 2.6 a Najeriya. Amma a halin yanzu wanda ake fitarwa bai kai Durum Miliyan daya ba.
A wani labarain kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashawa da cin hanci a gwamnatin baya ne ya hana sojojin Najeriya Murkushe yan kungiyar Boko Haram. Shugaban kasar ya bayyana wannan ne a fadar shugaban kasa a jiya.
The post Zamu kulle duka hanyoyin satar Mai – Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).