Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Май
2016

Yan Matan Chibok: Jam’iyyar PDP ta yaba ma soji

0

– Jam’iyyar PDP ta yaba ma sojojin Najeriya da suka tsiratar da daya daga cikin Yan Matan Chibok

– Ta zargi jam’iyyar APC da wasa da rayukan al’umma

Shugabannin jam’iyyar PDP a wani taron da sukayi kwanakin baya a Abuja

Jam’iyyar PDP ta yaba ma sojojin Najeriya da suka kubutar da Amina Ali, daya daga cikin yan matan Chibok da yan Boko haram suka sace.

An ceci Amina Ali ne a wani kauye wanda yake kusa da kasar Kamaru a ranar Laraba 18 ga watan Mayu na 2016. An same ta tare da Diyar ta da kuma mijinta, Muhammad Hayatu, wanda Kwamanda ne a cikin kungiyar ta Boko Haram.

KU KARANTA: 

jam’iyyar PDP kuma ta musanta zargin da jam’iyyar APC take yi mata na cewa Gwamnatin Jonathan bata sayi makamai ba inda ta bayyana a shafin ta na Twitter cewa, makaman da ake amfani dasu wajen yaki da Yan Boko Haram an saye sune a karkashin Gwamnatin Goodluck Jonathan ba karkashin shugaba `buhari ba kamar yadda jam’iyyar APC din ke da’awa.

Jam’iyyar PDP kuma tayi Allah wadai da yadda jam’iyyar APC a lokacin da take adawa ta ringa zuzuta wasu labarai domin ganin cewa ta kwace mulki daga hannun ta.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashawa da cin hanci a lokacin gwamnatocin baya ne ya sanya sojojin Najeriya ba su iya murkushe kungiyar Boko Haram ba. Shugaban kasar ya fadi hakannne a fadar shugaban kasa dake a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a jiya Laraba.

The post Yan Matan Chibok: Jam’iyyar PDP ta yaba ma soji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса