Ku karanta abun mamaki wanda wani fitaccen dan jarida ce game da Shugaba Buhari
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da magoya bayan da yawa a kasar Najeriya
– Akwai wani fitaccen dan jarida dake jihar Gombe mai suna Faruk Mu’azu ya rubuto kan tunaninsa da gwamnatin tarayya a karkashin Shugaba Buhari
– Ana kawo wani labari da sunan, sako da fatan alkairi ga Shugaba Buhari
Wani fitaccen dan jarida ya soma da hakan, muna fatan alkairi ga Shugaba Muhammadu Buhari bisa ga manufofin sa na alkairi ga al’ummar Nijeriya. Allah ya kare shi daga masu yi masa zagon kasa.
Shugaban kasar Najeriya mai suna Muhammadu Buhari
Muna so Shugaba Buhari ya yi duba ga halin da yankin mu na Arewa maso gabas ke ciki, mun shafe shekaru muna cikin hali na hau la’i. Mafiya yawan bangarori na jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba su iya noma abun da za su ci, don wasu bala’i ya sa sun tsallake mtsugunin su sun zama ‘yan gudun hijira. Yanzu mun dogara ne ga abun da jihohin Gombe, Bauchi da Taraba suka noma, Kuma su kansu jihohin uku abunda suka noman ba isar su zai yi ba balle ya hada da sauran yankunan.
KU KARANTA WANNAN: An nada mukaddashin shugaban hukumar shige da fice
Abunda nake kokarin bayyanawa anan shine ana matukar fama da yunwa a wannan yanki na shiyar Arewa maso gabas, ga halin da kasar ke ciki gaba daya.
Muna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari bisa hali irin nasa na tausayin talaka, da ya duba yankin da idon rahama wajen kawo dauki na gaggawa tare da ba mu fifiko na tallafi akan kowanne shiyya.
Wani fitaccen dan jarida dake jihar Gombe mai suna Faruk Mu’azu
A bangare guda kuwa yankin na fama da talauci fiye da kowanne shiya ga lalacewar hanyoyin sufuri da ilimi da sauran fannoni na rayuwa. A kasafin kudi na bana mun ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hanyar Gombe – Numan, muna godiya amma fa tsuguni ba ta kare ba don hanyar Biu zuwa Maidugri da Bauchi zuwa Gombe da Damaturu – Potiskum – Gombe suna lakume rayuka ba adadi. Muna fatan anan ma shugaba zai kawo gudumawa na gaggawa.
Shiyyar Arewa maso Gabas da ta kunshi jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, an jima ana maida ita saniyar ware amma yanzu lokaci ya yi da za a maida hankali akan ta ko don yanayi da jarrabawar da ta shiga ciki.
Da Fata shugaba Muhammadu Buhari da mukarraban sa zasuyi dubi akan wannan lamari. A karshe Ina kira ga gwamnonin shiyar, Dankwambo, Kashim, Bindo, MA, Darius da Geidam da su hada kai ba tare da bambancin siyasa ba domin tsamo yankin daga halin da take ciki.
Allah ya taimaki Buhari da Gwamnonin shiyyar Arewa maso Habas da Nijeriya baki daya.
The post Ku karanta abun mamaki wanda wani fitaccen dan jarida ce game da Shugaba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).