Ku karanta tsoratarwar labari da yan ta’addan Boko Haram ce game da yan matan Chibok
– Wani labari take fitowa ta bayyana wanda wata kungiyar masu hallaka suke cewa wanda kashi daya bisa uku na yan matan Chibok ba sa raye
– Amma guda biyu kawai ne an samu cikin wata matan Chibok
Yan matan Chibok wadanda yan kungiyar Boko Haram suke yi garkuwa da su tun watan Afirilu 2014
A wani mataki na karyata ikirarin daya daga cikin yan matan Chibok da aka ceto kwanaki, kungiyar Boko Haram Ta bayyana cewa kashi daya bisa uku na ‘yan Matan Chibok duk sun yi ‘shahada’.
KU KARANTA KUMA: An ba Gwamna Shettima daya cikin yan matan Chibok
Wannan bayanin ya fito ne daga jaridar ‘TIME’ ta Ingila wadda ta ruwaito wani kwamandan Boko Haram, Amir Muhammad Abdullahi na cewa a shirya suke su yi sulhu da gwamnati ta yadda za su sako sauran ‘Yan matan.
Ya kara da cewa idan har gwamnati Ta amince da sharuddan su, za su jingine makamansu.
Inda wasu yan Najeriya suke maganta kan hakan kan shafin Facebook. Na farko, Sabiu Abdullahi yace, Wai su jaridun ingila ah ina suke samu labarai daga wajensu kodai akwai Lauje cikin nadi ne ? Yakamata gwamnati ta duba wannan lamarin.
Wasu yan ta’addan Boko Haram
Na biyu, Bilyamin Musa Rafindadi yace, munafukan banza azzalumai karya suke sunyi laushine suna so gwamnati ta tsagaita musu wuta ne domin su samu damar sake sabon shirin cigaba da taaddanci Insha Allah bazaku samu nasara ba insha Allah sai sojoji sun ga bayanku makiya musulinci da musulmai.
Kuma, Moukhtar Sani Parooq yace, Hahah Bamu fatan Ayi sulhu dan Uwarku, Bayan kun gama kashe mana Yan uwa Da sunan Jahadi Tsinannu Uwaku xakuci va wata maganar sulhu.
The post Ku karanta tsoratarwar labari da yan ta’addan Boko Haram ce game da yan matan Chibok appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).