Sojoji sun kai al’ummar Ijaw hari, Buhari na kashe mutane kamar kaji – Kungiyar IYC
– Kungiyar Ijaw Youth Council (IYC) ta kai kukanta akan yawan kai harin da sojoji suke yi a jihar Ijaw – An zargi Shagaba Muhammadu Buhari akan ba da goyon bayan kashe kashe al’ummar Ijaw a cikin yankin – Kungiyar IYC sun bayyana cewa sojoji sun kashe mutane da yaw aba tare da dalili ba […]
The post Sojoji sun kai al’ummar Ijaw hari, Buhari na kashe mutane kamar kaji – Kungiyar IYC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
– Kungiyar Ijaw Youth Council (IYC) ta kai kukanta akan yawan kai harin da sojoji suke yi a jihar Ijaw
– An zargi Shagaba Muhammadu Buhari akan ba da goyon bayan kashe kashe al’ummar Ijaw a cikin yankin
– Kungiyar IYC sun bayyana cewa sojoji sun kashe mutane da yaw aba tare da dalili ba
– Kungiyar tayi kira ga al’ummar kasashen waje da su duba yadda ake kasha kasha a jihar Ijaw
Ya zo a bayani a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, Kungiyar IYC ta duniya tace tana da burin bayyana wa duniya akan yanda sojoji da kuma yadda ake aiwatar da kisan gilla ga mutan Ijaw da al’umomin yankin Niger Delta a Nijeriya.
Kungiyar IYC ta ce mutane mussaman mata da yara suna cikin hadari, idan ba’a kawo masu daukin gaggawa ba a yankin Gbaramatu na Jihar Delta.
Har yanzu ba’aga mafi yawan mutanan da suka gudu cikin daji a Oporoza, Kurutie, Kunukunuma, Kokodiagbene da sauran kauyuka da kuma al’umomin masarautar Gbaramatu a kudu maso yammacin karamar hukumar Warri na Jihar Delta ba.
Wannan ya hada da yanayin hana shiga da fitan daga sojoji a masarautar Gbaramatu.
Yawancin iyaye basu san inda yaransu suka shiga ba haka ma yaran basu san inda iyayensu suke ba
A wasu yankuna na Ogbe-Ijoh musamman a Naifor Island(makotan Warri), sojoji suna ta harbe harbe a daren 30 har zuwa 31 ga watan Mayu, a hukumomin wadda a tsarin wasu ma’aurata (mr and mrs Tiemo) suka jikkata.
KU KARANTA KUMA: An aika dakarun sojoji da ta murkushe Niger Delta Avengers
Kungiyar ta bayyana cewa babu matatan mai a Naifor Island, Ogbe-Ijoh, kuma babu a hukuma dake kusa da yankin. Saboda haka babu dalilin da zai sa sojoji suka yanke shawaran amfani da jihar a matsayin babban manufar gaskata makudan kudin da aka basu domin neman masu ramuwa.
Eradi yace: “Mutanen Ijaw sun kasance masu zaman lafiya, Mutanan Ijaw ba msu neman ramuwa bane, wadannan jiragen sama ne suka yawo a saman Yenagoa da kuma Gbaramatu, masu neman ramuwa ba a nan suke ba, muna kyautata zaton sun zo wucewa ne. yana nufin wani abu na shirin faruwa.”
Ya kuma bukaci Shugaba Buhari da ya kuma duba tsayuwar gwamnatin shi akan ci gaba da barazana da kuma amfani da karfin sojoji akan yan bindiga, a maimakon haka ya je Creek ya kuma tattauna da su.
The post Sojoji sun kai al’ummar Ijaw hari, Buhari na kashe mutane kamar kaji – Kungiyar IYC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.