EFCC ta kwato sama da 1 biliyan daga tsofaffin ministoci
– An dawo da Sama da naira biliyan 1 kudi a hannu da akayi amfani dasu ba bisa da doka ba a zaben 2015 zuwa cikin asusun hukumar hana al mundahana da yima tattalin arzikin kasa zaman kasa wato EFCC.
– Rahoto ya nuna cewa kudaden sun zo ne daga wasu tsoffafin ministoci,ma’aikatan hukumar zabe ,shuwagabannin jam’iyyar PDP da kuma wasu kungiyoyin kula da zabe.
– Kafin yanzu ma, hukumar EFCC ta daskarar da sama da naira biliyan 2 da ke asusun banki.
(EFCC)
Wata rahoto ta jaridar nation ,ta bayyana yadda aka dawo da sama da biliyan 1 asusun EFCC daga hanun ma’aikatan gwamnatin da ta ke tuhuma.
A game da rahoton, kudin na daga cikin naira biliyan 23.29 da ake zargin tsohon shugaban kasa goodluck ebele jonathan ya fitar dan yakin cin zaben shekaran da ya gabata.
A ruwaito cewan kudaden sun fito ne daga offishin tsohuwar ministan mai ,Mrs diezani Alison-madueke. Kuma har ila yau akwai alkawuran cewa za’a sake dawo da wasu biliyoyi, masaniyar tace.
Kudaden su shigo jiya ne 9 ga yuni, daga aljihun tsoffafin mistoci 2,ma’aikatan INEC 3,da kuma wani shugaban masu lura da zabe. Bugu da kari, sama da ma’akatan INEC 36 ne aka ambaci sunayensu cikin al mundahanan.
Wata masaniya da ta bada bayanai ta ce sama biliyan 1 ne wadanda suka raba kudin suka dawo da shi.
“A cikin duka sassan kasa guda 6, yawancin wadanda aka tuhuma sun gaskata cewa sun sha ko da romon haram din ne,binciken mu ya nuna mana cewa anyi wani usulubin raba naira miliyan 450 tsakannin jihohi 36 da birnin tarraya.
“wasu masu kashi a gindi sun dawo da kudin,bayan wasu sunyi alkawari,kuma wadansu kungiyoyin na ganawa game yanda zasu dawo da shi.
“a yanzu dai, mun kwato sama da biliyan 1 kudi a hannu,da kuma sama da biliyan 2 kudi a daskare a asusun banki a fadin kasa . Mun basu wa’adin lokaci,kuma da alamar suna da niyyan dawo dasu” masaniyar ta ce.
Masaniyar ta cigaba da cewa: “A cigaba da tuhumar da muke yi wa wasu ma’aikatan INEC a Maiduguri da kuma wasu tsofaffin ministoci 2, hukumar tabattar da hana cuta ta kamfanonin hake-hake da ta ke binciken ta kwato naira miliyan 62,750,000.
“Bincike na gudana akan al mamarin kuma zamu jiran aka wasu domin amsa tambaya. Ma’aikatan INEC din kuma na daure a ofishin EFCC”.
“A yanzu dai ,sama da ma’aikatan INEC 36 sun amsa tambayoyin mu kuma bamu gam aba, muna jiran Karin sunaye daga ofishin mu a fatakwal,enugu,gwambe,kano,da legas.
“A karshe,zamu tura tsarin sunayen zuwa ga INEC domin gurfanar da su .
“Wannan fa ba ha’inci, wasu ma’aikatan sai sun gurfana akotu,” masaniyar ta kare.
A halin da ake ciki, tsohon shugaban jam’ian sojojin sama, Iya Mashal Muhammad Umar(mai ritaya) ya gurfana a gaban kotun shari’a zunubai 7 na satan kudi da EFCC ta kai kara.
Iya mashal Muhammad umar(mai ritaya),shine tsohon shugaban jam’ian sojojin sama na Najeriya tsakanin watan Satumba 2010 da Disamba 2012,kafin Alex Badeh.
The post EFCC ta kwato sama da 1 biliyan daga tsofaffin ministoci appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.