Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июнь
2016

Zamu kai hari ga gwamnoni – ‘Yan bindiga

0

– Wata kungiyar ‘yan bindiga tayi barazanar kai hari ga duk gwamnan neja deltan da yake kokarin zama cikas ga gwagwarmaya da sukeyi a yankin

-Sabuwar kungiyar ‘yan bindigan tayi bayanin dalilin da yasa ta fasa harba harsashai masu linzamin da tayi barazanar harbawa

Yan bidiga dadi

Kuniyar hadakan kwato yancin yankin neja delta wato ‘Joint Niger Delta Liberation Force’ tayi barazanar kai hari ga gwamnonin yankin neja deltan da ke tunanin yaudaren su. Tayi gargadin cewa zata kai mumunan hari ga duk gwamnan yankin da yake kokarin zama cikas ga gwagwarmayan da suke yi, game da jaridar Vanguard.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama wani jigon APC

A kullun,‘yan bindigan na kai hare hare kafufuwan mai,  wanda  hakan ne dalilin saukar sarrafa man fetur na kasa da kuma rashin wutan lantarki a kasa ga baki daya. Barazanar ta zo ne bayan kwanaki kalilan da suka kai hari wata kafan mai a garin Ogidigben, karamar hukumar Warri kudu maso yamma ta Jihar Delta.

A Ranar Juma’a ne,wata sabuwar kungiya mai suna ‘Voice Delta’ tayi ikirarin cewa itace ummul khaba’isin da ya hana zaman sulhun da gwamnatin tarraya ta ke shiryawa da tsagerun Neja Delta. A wani sabon jawabi,kungiyar yan bindigan ta hanyar Janar Akotebe Darikoko, Kommandan ayyuka na ranan juma’a, ya bayyana dalilin da yasa basu jefa  harsashai masu linzamin da sukayi barazanar harbawa ba.

Duk da cewa ta yi alkawarin sulhu da gwamnatin tarayya, kungiyar ta mika bukatunta 7 da zai tsagaitar da hara haren.

“Zamu cigaba da zaman sulhun har sai an biya bukatun mu.

“Wakilan mu na sulhun,musamman gwamnonin yankinmu ba zasu yaudare mu ba.

“Duk wanda kuma ya yaudare mu a cikinsu,toh ya yaudare yankin mu gaba daya kuma sai mun kai masa hari,” ‘yan bindigan suka fada.

The post Zamu kai hari ga gwamnoni – ‘Yan bindiga appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса