Hukumar EFCC ta kama wani jigon APC
Hukumar hana cin hanci da rashawa ta kasarnan watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta kama Alhaji Abdullahi Adamu a bisa zargin cin hanci da tattara dukiyar haram.
Shugaban hukumar EFCC
Kamfanin labarai na PM ya ruwaito cewar Abdullahi Adamu dai tsohon dan takara ne na gwamna a garin Bauchi karkashin jam’iyyar APC kuma an gurfanar da shi ne a gaban wata kotu dake garin Jos jihar Plateau.
KU KARANTA: Masu fada da Sheriff
Shidai Abdullahi Adamu din an gurfanar da shi ne tare da kamfanin sa na Solid Unit Nig. Ltd gaban alkali Yakubu Dakawak jiya Alhamis. Tuni dai Abdullahi Adamu din ya karyata zargin da akeyi masa inda kuma mai karar ya bukaci da kotu tasa a kulle shi.Mai shari’a Dakawak din dai ya dage sauraron karar har zuwa yau juma’a sannan kuma ya bada umarnin ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari kafin sauraron belin sa.
A wani labarin kuma tsohon gwamnan jihar Enugu Sullivan Chime ya shiga hannun hukumar EFCC din a ranar laraba saboda sa hannun shi a wata badakala har ta N23 biliyan da tsohuwar minista Diezani Madueke ta yi.
The post Hukumar EFCC ta kama wani jigon APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.