Yadda muka kashe kanal sama’ila inusa-abun zargi
– Babban abun zargi da kisan kanal sama’aila inusa ya bayyana yanda suka aikata ta’asan.
– Emeka yace basu yi nufin kashe kanal din ba, innama motarsa kawai suka yi nufin kwacewa.
– Sun harbe shi ne a yayin da yake gwagwarmayan kwatan kansa.
Sojojin Najeriya
Babban abun zargi da kisan kanal sama’ila inusa ya nanata abunda ya faru, jaridar Sun ta ruwaito. An sace inusa ne a gaban matarshi ranar 26 ga watan maris a jamsin NNPC dake jihar kaduna, an tsinta gawar bayan kwanaki biyu da batarsa.
Abun zargin,emeka ya bayyana cewa ko da kadan basu yi nufin kashe kanal din ba , innama motarsa kawai suke bukata. Yace inusa ya kwace bindigan daya daga cikinmu ,a yayin yunkurin kwatan bindigan ne muka harbeshi.
KU KARANTA: Yadda Abba Moro ya yaudari mutane
Emeka ya kara da cewa sun sayar da motan naira 800,000.
“A ranar lahadi ne da yamma, muna fatrol;duk motan da muka gani zamu kwace. a lokacin ne muka ga motar kanal ta fito daga kwalegin ‘yan sanda ta gangaro jamsin kamfanin tatan mai(rifanare), sa muka far masa muka kwace.
“Da wuri muka mika wa dan-sokoto ya tafi da ita. Daga baya, muka kaishi hanyan Abuja muka ce mai ya kwanta ya kwantar da hankalinshi saboda motarshi kawai muke bukata,ba rayuwarshi ba.
“Na fada masa; ka fi karfin wannan motan,kuma zaka iya siyan wata. Jim da kadan,sai yace yana bukatan ruwan sha,sai na je mota na kawo masa ruwa. Tsugunawana ke da wuya sai ya zare bindiga ta ya cire gidan harsashin.
“Amma akwai ragowar harsashi daya a ciki, shi ya rike bindigan ,ni na rike bakin bindigan, mun ta gwagwarmaya,da na lura yana nufin harbi na sai na juya bakin bindigan wurin sho, sai ya harbi kansa.
“Na fada masa, bamuyi niyyan kashe ka ba gashi ka kashe kanka. Amma fa kiris ya rage da ya kashe ni”
“Bamu san soja bane, sai bayan mako daya da faruwan abun muka fara gani a jaridu da kafafun yada labarai cewa wani babban jam’in soja muka kashe. Mu sana’ar mu kwacen mota,ba satan mutane ba” ya fada.
Offishin ‘yan sanda ta jihar Kaduna tare da Insfecta janar na ‘bangaren jinsin masu fasaha da ceto sun bibiyesu kuma suka kama su. Kamuwarsu ta yiwu ne a yayinda bangaren jinsin masu fasahan suka samu siginar wayan kanal sama’aila wani ma’aikacin kurkuku,Abdullahi adamu na amfani da ita , ashe abokin aikin makasan ne.
The post Yadda muka kashe kanal sama’ila inusa-abun zargi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.