Okorocha na shirin kwace kungiyar gamayyar yan Ibo
Ana zargin gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha na wan shiri domin kwace kungiyar gamayyar yan ibo ta Najeriya kafin zabe mai zuwa.
Gwamna Rochas Okorocha
A wata tattaunawa da jaridar Vanguard tayi da Okechuku Isiguzoro wanda kuma shine shugaban matasa na wannan kungiyar gamayyar yace gwamnan ma dai shine yake daukar nauyin gina hedikwatar kungiyar da akeyi a garin Enugu.
KU KARANTA: Daukar Ma’aikatan NIS, Yadda Abba Moro ya yaudari mutane
Isiguzoro ya cigaba da cewa shugaban kungiyar na yanzu ya ki sauka akan mukamin sa duk kuwa da cewa wa’adin sa ya wuce saboda yana son ya mika ma wani daga jihar Imo ne kujerar duk kuwa da cewa ba haka tsarin ya kamata ace yake ba.
A yadda tsarin ya kamata ya kasance dai shine shugaban kungiyar na yanzu wanda ya fito daga jihar Ebonyi kamata yayi ya ba dan jihar Enugu mulkin amma shi gwamna Okorocha yana so ne a ba wani yaron nashi daga jihar Imo shugabancin don wata manu fa tashi kafin zabe mai zuwa.
Shugaban matasan kuma ya kara da cewa yadda shuwagabannin kungiyar gamayyar ke zuwa gidan gwamnatin Imo ya isa ya zama shaidar hakan. A farkon watan nan daine aka wayi gari an lika hotunan gwamnan na jihar Imo da na jihar Borno a jihar Imo din a matsayin yan takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.
Amma daga bisani kuma gwamna Rochas din ya fito ya nisan ta kanshi da hotunan.
The post Okorocha na shirin kwace kungiyar gamayyar yan Ibo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.