Tsagerun neja delta sun sa wa gangar man Agip bam
– Tsagerun neja delta sun sa wa gangar man kamfanin Agip da ke obi obi brass bam.
– Sun kai harin ne da kimanin karfe 3 na safiyar yau,10 ga watan yuni.
Tsagerun Nija Delta
Kungiyar tsagerun neja delta ta ce it ace da alhakin sa bam a gangar man kamfanin Agip da obi obi brass. Kungiyar ta bayyana hakan ne ta shafin su na twita cewa gangar da suka sanya wa bam,na daga cikin manyan gangunan Agip da ke jihar Bayelsa.
KU KARANTA: Kisan batanci; Yan sanda sun gurfanar da mutane 5
Ku tuna cewa kungiyar ta ki tattaunwa da gwamnatin tarayya duk da gwamnati ta janye sojojin ta daga yankin neja delta. Kungiyar ta bayyana cewa ta ji dadin cewa kamfanonin tatan mai na kasashen waje sun daina siyan man najeriya.
Tsagerun neja deltan sunyi alwashin sai ta nakasa sarrafa man najeriya,kuma bata gushe tana yiwa kamfanonin mai gargadin cewa kada su gyara gangunan da da suka sanya wa bam. Ku tuna, al’amari ta nuna cewa najeriya tayi hasaran kimanin dala miliyan6.72 ta dalilin tabargazan da tsagerun neja delta keyi.
The post Tsagerun neja delta sun sa wa gangar man Agip bam appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.