Daukar ma’aikatan NIS:yadda abba moro yayi kunnen kashi
– Tsohon Komftrola janar na ma’aikatar kula da shiga da fice ta najeriya, David Parradang yayi bayani wa babban kotun tarayya yadda aka kwace wasikokin daukan aiki sabanin umurnin tsohon shugaba Goodluck Jonathan
– Yace a lokacin, Abba Moro ne Ministan ma’aikatar cikin gida
– Parradang yayi bayanin cewa ma’aikatar cikin gida tace daukan aikin da akayi ba bisa doka bane
Tsohon komftrola janar na ma’aikatar kula da shiga da fice ta Najeriya,David Parradang ya fada wa wata babban kotun tarayya yadda gwamnatin tarayya ta yaudari wadanda hatsarin ranar horon daukar ma’aikatan ma’aikatar shiga da fice ta shafa a shekarar 2014.
A bada shaidar da yayi a yau,10 ga watan yuni, Parradang ya bayyana cewa tsohon minIstan Abba Moro ya kwace wasikokin daukan aikin da aka ba mutane 45 (uku uku daga cikin dangin mutane 15 da suka rasa rayukan su).
KU KARANTA: Yan sanda sun gurfanar da wadanda ake zargin su da kisa
“ Basu wasikar ke da wuya, ma’aikatar cikin gida ta aiko da sakon su dawo da wasikokin,” ya fada
Parradang ya kara da cewa a yayinda aka ma’aikatar(karakashin abba moro) ta amince da wadanda aka dauka a mastayin kananan ma’aikata, tayi watsi da wadanda aka dauka a matsayin manyan ma’aikata.
Duk da hakan, bai bada adadin kananan ma’aikatan da aka dauka ba. Tsohon shugaban kasan ya bada aiki kai tsaye ga wadanda suka raunana da kuma dangin wadanda suka rasa rayukan su a ranan yin horon daukan aikin.
Paradang ya sake jaddadawa kotu cewan adadin mutane 15 ne suka rasa rayukan su a ranan.
“Bayan aukuwan hatsarin, mutane 15 ne suka rasa rayukansu tare mutane 165 da suka ji raunuka iri iri a duk fadin kasan gaba daya.” Ya fada wa kotu.
Mai bada shaida na farko a taron gurfanar da abba moro da wadansu 3 yace, ma’aikatan cikin gida(karkashin jagorancin abba moro) ce ta karba kudade a hannun masu neman aikin shiga ma’akatar kula da shiga da ficen.
A shaidar da ya bada a yau, tsohon komftrolan ma’aikatar kula da shiga da fice ta kasa,David Parradang yace an fada mai kudaden da kamfanin fasaha ta dextral ta tara na horon a 2015,kawai na ayyukan yanar gizo ce.
Mai bada shaidan yace babu wani sadarwa tsakanin shi da ma’akatar akan horon daukan aikin sai watan yanaya 2014.
The post Daukar ma’aikatan NIS:yadda abba moro yayi kunnen kashi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.