An zargi NAFDAC kan shigowa da tumatur din gwangwani
An zargi hukumar kula da daidaito na abin ci da magun guna na kasar nan watau National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC) bisa shigowa da akeyi da tumatir din gwangwani mai kisa daga kasashen waje. Kungiyar masu tumatir din yan Najeriya ne suka yi wannan zargin a wani taro da sukayi da yan kwomitin lafiya na majalisar tarayya a Abuja.
Abubuwan da hukumar take amshewa
A wurin taron dai an bayyana kasar China da India a matsayin kasashen da ake shigowa da tumatarin mai kisa. Shugaban kamfanin Erisco Eric Umeafia ma dai yadora alhakin shigowa da tumatarin kacokan kan NAFDAC din inda yayi kira da a a jama su kunne.
Shima dai shugaban kamfanin Dangote na Tumatir Abdulkarim Kaita din ya goyi bayan takwaransa na Erisco inda ya kara da cewa sun kasahen na China da India din basu anfani da tumatir din amma sai su kawo shi nan.
Shi kuma wakilin NAFDAC din a wajen taron ya karyata zancen nasu inda ya bukace su da su rika tabbatar da magana akafin su fade ta.
The post An zargi NAFDAC kan shigowa da tumatur din gwangwani appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.