Kisan batanci: ‘yan sanda sun gurfanar da mutane 5
‘Yan sanda sun gurfanar da mutane 5 a gaban wata kotu a Kano bisa zargin kisan Bridget Agbahime wacce aka ce ta zagi Manzo
Jami’an yan sandan Najeriya
Baya ga kisan kai, ana kuma tuhumar mutanen da ta da zaune tsaye. Ana zargin Dauda Ahmed da jagorantar sauran wadanda ake zargi wajen yin kisan matar tare da sassara ta.
Kisan gillar da aka yi wa matar a Kofar Wambai a Kano ya fusata al’ummar Najeriya.
KU KARANTA: Shugaban kasa yayi waya da Osinbajo daga Landan
Shugaba Muhammadu Buhari da gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma sauran jama’a sun yi tir da wannan aika-aika sun bukaci da a hukunta wadanda suka yi wannan danyen aiki. A ranar Junma’a 10 ga watan Yuni ne aka gurfanar da wandan da ake zargi a gaban kotu a Kano a bisa zargin kisan yin batanci ga Manzan Allah mai tsira da aminci.
A cewar ‘yan sanda, ana zargin Misisi Agbahime da zagin Annabi wanda hakan ya sa aka yi mata dukan da ya kai ta har lahira. Wadanda ake zargi Dauda Ahmed, da Abdullahi Mustapha, da Zubairu Abubakar, da Abdullahi Abubakar, da kuma Musa Abdullahi, an gurfanar da su ne a gaban wata kotun Majistire a cewar Premium Times. Idan aka same su da laifi za’a yanke musu hukuncin kisa.
A lokacin da ake sauraron karar Dauda Jibrin mai gabatar da kara ya ce, a ranar 2 ga watan Yuni da misalign karfe 4:00 na yamma Ahmad ya je wurin marigayiya Agbahime bayan ya mare ta sai ya yi kabbara da niyyar tada da hargitsin addini.
Sannan sai Abdullahi Mustapha da Zubairu Abubakar suka zo wurin tare da Salawiyu da Ibrahim da Dini da Isiaku Mada da Malam Sani da Yunusa Sufi wadanda ake nema ruwa a jallo a inda suka cincirindo a shagonta da ke kasuwar.
Suka kuma yi mata dukan tsiya da sanduna a inda suka ji mata mummunan rauni wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta. Wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake yi musu, yayin da Mustapha da kuma Abubakar suka ce sa ba wurin da aka aikata laifin. An daka sauraron shari’ar har sai ranar 28 ga watan Yuni domin ba ‘yan sanda damar kammala bincike.
The post Kisan batanci: ‘yan sanda sun gurfanar da mutane 5 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.