Labari da dumi dumi: Shugaba Buhari yayi kiran bidiyo da mataimakin sa
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da rahoton cewa yayi kiran bidiyo tare da mataimakin sa
– Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana haka ta shafin sadarwan ta na Twitter daga Swith Magazine.
– Shugaban na Najeriya yace ya na cikin koshin lafiya kuma yana mika godiya ga yan Najeriya da irin addu’oin su gare shi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Anyi gani na karshe ga shugaban kasa a kwanaki biyar da suka wuce, Litinin, 6 ga watan Yuni, a filin jirgi na Nnamdi Azikwe International Airport dake birnin tarayya Abuja. Shugaban kasan Najeriya ya tafi hutun kwana goma a garin Landan domin ya huta da kuma ganin likita a kan kiwon lafiyar sa.
KU KARANTA: Kamfanin MTN ya amince zaya biya BiliyanN333
Shugaba Buhari wanda a gwargadon rahoto yana da wani cuta a kunne, wani likitan sa na sirri tare na gwani a E.N.T sunyi nazarin ciwon kuma sun magance cutan a birnin tarayya Abuja. A halin yanzu, likitocin guda biyu sun shawar ce shi da ya kuma ganin likita a kasar waje a matsayin rigakafi.
Damuwa akan lafiyan shugaban kasa yayi girma, bayan ya soke tafiya zuwa gurin arzikin man petir na Niger Delta a makon da ya gabata. Ana sa ran zai dawo kasar a 16 ga watan Yuni.
The post Labari da dumi dumi: Shugaba Buhari yayi kiran bidiyo da mataimakin sa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.