Labari da dumi dumi: kamfanin sadarwa ta MTN ta amince zata biya naira biliyan N333
-A karshe MTN sun amince zasu biya naira biliyan N333 daga cikin biliyan N780 na harajin da gwamnatin tarayyan Najeriya ya daura masu
-Za’a biya harajin ne a na tsawon shekaru uku
Kamfanin sadarwa na MTN, a karshe sun yarda da biyan naira biliyan N333 daga cikin biliyan N780 na harajin da gwamnatin tarayyan Najeriya ya daura masu.
A cewar kamfanin sadarwan na MTN, zasu biya harajin ne tsawon shekaru uku.
KU KARANTA: An saka Bam a Obi Brass Truck line
ku tuna cewa, gwamnatin tarayya ta saka takunkumi ga MTN akan kin bin umarnin cire layuka miliyan 5.1 da ba’a yi rajista bisa ka’ida ba. Kamar yadda yake a wani bangare na magance tsarin, kamfanin sadarwa na MTN sun sanar da cewa, zasu tabbatar da tsara sunayen hannun jarinsu a ma’ajin musayar Najeriya.
Chiyaman na kungiyar MTN a cikin wasikar ajiye aikinsa yace: “An mayar da kuma karfafa dangantaka dake tsakanin Kamfanin sadarwan MTN, Gwanatin Najeriya, da kuma kungiyar Nigerian Communication Comission.” Kafin ya ajiye aiki, shi ya jagoranci tsarin shawarwari tare da gwamnatin Najeriya
The post Labari da dumi dumi: kamfanin sadarwa ta MTN ta amince zata biya naira biliyan N333 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.