Wutar Lantarki: fashola ya koka da tsageru
-Ministan ma’aikayar lantarki da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola babu wanda ya fi shi rashin kwanciyar hankali a yanzu
-Rashin tabuka komai a yanzu sun shafe nasarorin da Fashola ya samu a Legas lokacin da ya ke gwamna
-Ministan ya samu damar bayani kan irin halin da ya ke ciki a yanzu
Fashola
Ministan lantarki da ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ya dora alhakkin rashin samun wutar lantarki da ake fama da shi a fadin kasar a kan fasa bututun mai da tsagerun Naija Delta ke yi.
Fashola wanda ke magana wani taron tattaunawa da al’umma kan nasarorin gwamnatin Buhari a Abuja a yau, 9 ga watan Yuni, wanda Cibiyar Dimukuradiyya da Ci gaban kasa ta shirya a Abuja, ya ce: “ban san wata kasa da ke son amfani da wutar lantarki amma kuma ta rika lalata abubuwan samar da wutar ba irin Najeriya.”
Ya kuma ci gaba da cewa “kwarai babu wutar lantarki, amma ba hakan na nufin babu hanyar da za’a samar da shi ba. A watan Fabarairu mun samar da megawatt 5,000. ”
“Za ku yi mamakin yawan adadain bututun mai, da kuma yadda suka ratsa cikin kasar nan”.
KU KARANTA: Jama’a na taya iyalin Keshi jimami
Minista Fashiola ya tabbatar wa da masu sauraronsa a taron cewa burin wannan gwamnati shi ne ta samar da kimanin megawatt na lantarki 20,000 a shekara 5.
Ya kuma yi Magana kan tsare-tsaren samar da wutar lantarki ta wasu hanyoyin da ban wandan da ba na mai ba, da kuma kare kadarorin gwamnati.
“Akwai lokacin da zai zo da ba za mu iya dogaro da iskar gas kadai ba, mu na masu ra’ayin cewa tsare-tsare da salo da kuma hada hannu za su kai mu inda mu ke so mu je”.
“Dangane da batun tsaro kuma, a yanzu wani zamani ne da Allah Ya kawo mu na yawaitar aikata muggan laifuka a duniya baki daya. Tsarin da ake da shi na maganta irin wadannan tun yakin duniya sun yi tsa-tsa, sai an sake sabon karatu. A cewar Ministan.
Kan batun cewa aiki yayi mi shi yawa ganin cewa yana kula da ma’aikatu uku manya a kasar. Fashola ya kwatanta wadannan ma’aikatu da gwamnati jihar Legas yana mai cewa wannan bai taka kara ya karya ba.
Ga kalamansa: “Na rike manyan ma’aikatu 30 da kanana 57 a Legas. Banbancin kawai shi ne sabbin mutanen da na ke aiki da su wandanda kuma mu ke karuwa da juna”.
“Ai kamar wasan kwallo ne da sabbi ‘yan wasa, wannan ba bu komai ganin cewa ina da kwararrun ma’aikata da kuma masu ba da shawara”.
A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ta soma bincike kan yiwuwar cewa wasu kasashe na bayan tsagerun Naija Delta Avengers. Ana rade-radin cewa bangaren leken asiri na rundunar soji tare da hukumomin jami’an tsaro na Najeriya sun kaddamar da wani bincike na gano inda tsagerun ke samun manya makaman da suke amfani da su.
The post Wutar Lantarki: fashola ya koka da tsageru appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.